Aminiya:
2025-07-31@16:52:03 GMT

NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya

Published: 20th, April 2025 GMT

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi.

Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas

Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini.

NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai kayayyakin zuwa Saudiyya.

Baya ga haka, hukumar ta NDLEA ta yi ƙarin bayani game da wasu jerin nasarori da ta samu a makon da ya gabata a ƙoƙarin da take yi na daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi.

A wani kamfanin na daban da ke jigilar kayayyaki, hukumar ta NDLEA ta ce ta kama kilo 2.8 na tabar wiwin Loud wadda aka shigar da ita ƙasar daga Amurka.

A Kano, jami’an NDLEA sun kama wani matashi ɗan shekara 22 da haihuwa da ke sayar wa ‘yan fashi da haramtattun kayayyaki a lokacin da suke sintiri a hanyar Bichi zuwa Kano.

An kama matashin ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilun, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Katsina ɗauke da kwalabe 277 na allurar pentazocine a ɗaure a cinyarsa da kuma cikin al’aurarsa.

Haka kuma, an kama wani da ake zargi mai suna Mohammed Abdulrahman Abdulaziz, mai shekaru 43, a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Rimin Kebe da ke Nasarawa a Kano tare da sunƙin wiwi nau’in skunk 68, wanda nauyinta ya kai kilo 30.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hodar iblis Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026.

IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.

Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa

Asusun ya yi hasashen samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu.

Haka kuma, IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samun ƙarin bunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.

Sai dai duk da wannan, wani rahoto IMF ya fitar a watan Yunin bana, ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya.

IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki.

A cikin kasashe 189 da aka gudanar da bincike a cikinsu, Nijeriyar na a mataki na 178, inda ta zarta kasashe irin su Yemen da Sudan ta Kudu da Kwango da Nijar da Sudan, wadanda kusan dukkaninsu ke fama da rigingimu a halin yanzu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
  • Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
  • Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
  • Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja