Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a Zamfara
Published: 3rd, May 2025 GMT
Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara.
Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis.
Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma.
Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga biyar da wasu da dama.”
Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano da wasu 4Ya ƙara da cewa sojojin sun bi sawun ’yan bindigar da suka tsere inda suka ƙwato manyan bindigogi guda shida da bama-bamai da kuma harsasai iri-iri.
Washegari kuma a yayin da sojojin ke ci gaba aiki, mazauna yankin sun mika musu wasu ƙarin makaman da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
Kyaftin Omale ya bayyana cewa fararen hula biyu sun samu raunin harbi a yayin musayar wuta amma suna samun kulawa a asibiti, a yayin da ake ci gaba a aikin gamawa da ragowar ’yan ta’addan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Arangama jagororin yan bindiga musayar wuta Zamfara yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa.
A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar ta amince da matakin ne bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa kan laifukan jarabawa na jami’ar.
Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da ɗalibai biyar na tsawon shekarar karatu biyu, tare da soke duk jarabawarsu da laifin ya shafa.
Jami’ar ta kuma jaddada cewa ba za ta lamunci aikata laifukan jarabawa ko rashin ɗa’a ba.