Babu Wata Suka Da Za Ta Hana Gwamna Dauda Lawal Aiwatar da Ayyuka.
Published: 21st, April 2025 GMT
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa babu wani kamfen batanci da zai hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da sadarwa na gwamna, Malam Salihu Nuhu Anka ya rabawa manema labarai a Gusau.
A cewar Anka, Gwamna Lawal ya fara aiki ne a wani aikin ceto, kuma tuni mazauna jihar suka fara cin ribar dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan kalaman da ya bayyana a matsayin maras tushe da wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya yi, yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya kalubalanci kalaman da Gwamna Lawal ya yi a wata hira da ya yi da shi kwanan nan.
“A yayin taron manema labarai, Dosara ya kai wa Gwamna Dauda Lawal hari cikin rashin kunya a kokarinsa na burge tsohon Gwamna Bello Matawalle,” Anka ya yi zargin.
REL/AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar.
Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci.
Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku.
Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace.
Ya kara da cewa, “Kasancewar manyan jami’an Nijar a taron da kuma kwamitin hadin gwiwa wani mataki ne mai ban sha’awa na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.”
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa, bunkasa alaka da Nijar abu ne mai matukar muhimmanci, “idan aka yi la’akari da matsayinta kan ci gaban yanki da na kasa da kasa da kuma ra’ayi daya kan batutuwan Falasdinu da Lebanon.”
A yayin da yake tsokaci ga kiran da ministan na Nijar ya yi na inganta alaka a fannin noma, man fetur, da makamashi mai dorewa, Aref ya bayyana wadannan fannoni guda uku a matsayin muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar Iran da Nijar, wadanda ya ce kwamitin hadin gwiwa zai duba su.
Yayin da yake tsokaci kan dangantakar tattalin arziki, ya ce, ya kamata kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu su zuba jari don ciyar da matakin hadin gwiwa zuwa matsayi mafi girma.