Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Bada Tallafin Kudi Ga Manoman Alkama
Published: 20th, April 2025 GMT
Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Uba Builder, ya sake jaddada kudirinsa na kyakkyawan shugabanci wajen gudanar da harkokin karamar hukumar.
Ya bada wannan tabbaci ne yayin rabon Naira dubu hamsin hamsin ga mutane 70 da suka amfana da shirin noman alkama da karamar hukumar ta kirkiro.
A cewarsa, mutane 165 ne aka saka cikin shirin, inda matasa 70 daga ciki ‘yan siyasa ne, wadanda a ke da bukatar canza rayuwarsu zuwa hanyoyin neman na kai, duba da cewa siyasa ba sana’a ba ce, illa tsarin shugabanci ne.
Alhaji Muhammad Uba Builder ya ce an samar wa mahalarta shirin da filin noma, tare da gyaran filin, da samar da irin alkama da sauran abubuwan bukata, yayin da suke lura da gonakin har zuwa lokacin girbi.
Ya ce kasancewar wadannan ‘yan siyasa sabbin shiga harkar noma ne yasa ba su samu gagarumar nasara ba, don haka akwai bukatar a kara tallafa musu da jari domin su shiga kananan sana’o’i, yayin da karamar hukumar za ta hada kai da hukumar manoma da makiyaya domin samar musu da kadada daya ta noma ga kowanensu domin su yi noma na damina.
Shugaban ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jita, su kasance masu juriya, da addu’a ga shugabanni domin su gudanar da aikinsu bisa adalci da gaskiya.
Da suke magana a madadin ‘yan siyasa, Usman Sarki da Bello Ajayi sun sake jaddada kudurinsu na kare mutuncin jihar da shugaban karamar hukumar tare da alkawarin shiga harkokin da za su inganta rayuwarsu ta tattalin arziki.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa karamar hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA