Aminiya:
2025-11-03@09:58:30 GMT

Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa

Published: 8th, April 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata sun kai harin ɗaukar fansar kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Kachalla Isuhu Yellow da aka fi sani da Ɗan Isuhu.

’Yan ta’addan sun kai harin ne ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, domin ɗaukar fansar kashe jagoransu da jami’an tsaro suka yi makonni biyu da suka gabata.

Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58

Mazauna sun ce maharan sun kashe mutum ɗaya yayin da suka ƙone motoci 11 sannan kuma suka wawushe kayayyaki a kantinan ’yan kasuwa a yayin harin.

Bayanai sun ce ana zargin ’yan ta’addan da suka kai wannan hari mayaƙan Adamu Aliero ne — yayan marigayi Ɗan Isuhu.

Kachalla Yellow wanda ake alaƙantawa da kai munanan hare-hare a Zamfara da kuma babbar hanyar Funtua zuwa Gusau, ya gamu da ƙarshensa ne a yayin wani artabu da wata rundunar haɗin gwiwa ta Asakarawan Zamfara da kuma jami’an ’yan sanda a ƙauyen Keta.

A yayin da wasu rahotanni ke cewa, Ɗan Isuhu ya yi gamo da ƙarshensa ne a hannun wasu ’yan ta’adda masu adawa da shi da ke yi wa Dogo Gide mubaya’a, wasu kuma na cewa dakarun soji ne suka kawar da shi daga doron ƙasa.

Wani mazauni Danjigba — wani yanki da ke makwabtaka da Keta — ya tabbatar da cewa an kashe Isuhu Yellow ne a yayin da yake yunƙurin yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa ƙauyen Keta domin kai ɗauki.

“Shi da mayaƙansa sun yi ƙoƙarin yi wa jami’an tsaron kwanton ɓauna amma a yayin musayar wuta da su aka kashe shi tare da mayaƙansa da dama.”

Ya ƙara da cewa, ragowar ’yan ta’adda a hanyarsu ta tserewa sun kai wa mazauna Danjigba hari, inda suka kashe mutum takwas ciki har da wani ɗan uwansa da wawushe kuɗi a hannun ’yan kasuwa.

Duk da aukuwar wannan hari, sai dai mazauna suka yi murnar mutuwar Isuhu Yellow, suna masu bayyana shi a matsayin marar imani wanda ya ɗauki alhakin sacewa da zubar da jinin mutane da dama a Tsafe, Gusau, Dan Sadau da kuma Funtua.

Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kashe Isuhu Yellow a wani aikin haɗin gwiwa na jami’an tsaro da suka daƙile harin da aka kai ƙauyen Keta.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m