Aminiya:
2025-10-13@15:49:43 GMT

An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano

Published: 23rd, March 2025 GMT

Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla.

Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin masarautar.

Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe

Lamarin ya ɗauki sabon salo ne, bayan wata wasiƙa daga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya fitar kan shirinsa na yin hawan salla a bana.

Wasiƙar, wacce sakataren Sarkin, Abdullahi Haruna Kwaru, ya sanya wa hannu, an aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, inda ya bayyana shirinsa na gudanar da hawan salla.

Daga cikin hawan da ya bayyana cewar zai yi akwai Hawan Daushe, da Hawan Nassarawa a ranakun 2 da 3 ga watan Shawwal 1446 bayan hijira.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da ya fara shirin gudanar da hawan salla.

A cikin wasiƙarsa, Aminu Ado, ya ce wannan hawan na da muhimmanci a gare shi saboda zai cika shekarj biyar da zama sarki.

An jima ba a gudanar da bikin hawan salla ba a Kano saboda fargabar abin da ka iya faruwa tsakanin mabiyan sarakunan biyu.

Rikicin ya fara ne bayan da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe Sanusi II daga sarauta, tare da naɗa Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano.

Sai dai a shekarar 2024, Majalisar Dokokin Kano, ta sake sauya dokar masarautar tare da rushe dukkannin masarautu biyar da Ganduje ya ƙirƙira, tare da mayar da Sanusi II a matsayin Sarki.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da tashin hankali a jihar, lamarin da ya sanya tsagin Aminu Ado tafiya kotu.

Kotu ta yanke hukuncin cewa komai ya ci gaba da zama a yadda yake har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yanke hukuncin ƙarshe, lamarin da ya sa dukkanin ɓangarorin biyu ke iƙirarin suna da iko a kan sarautar.

Har yanzu, gwamnatin Kano da Sanusi II ba su ce komai ba kan wasiƙar da Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda, kuma har yanzu ba a ji ta bakin rundunar ’yan sandan jihar ba.

Sai dai, jama’a na nuna damuwa kan abin da ka iya faruwa.

Malam Haladu Bello, wani dattijo mai shekaru 78 a duniya, ya bayyana damuwarsa kan cewa lamarin zai iya haifar da rikici.

“Na sha ganin hawan salla mai ƙyatarwa da kuma wanda ke da matsaloli, amma wannan yana da ban tsoro.

“Abin takaici ne yadda shugabanninmu ke watsi da hatsarin da jama’a ke fuskanta.”

Wani matashi mai shekaru 30, Alhaji Usman Shehu, ya bayyana cewa wannan rikicin cikin gida ne, ba wai abu ne da zai sa mutane cikin fargaba ba.

Ya ce: “Kullum cikin fargabar abin da zai biyo baya muke. Wannan ba daidai ba ne. A bar mu, mu more al’adunmu cikin zaman lafiya.”

Yayin da bikin salla ke ƙara ƙaratowa, al’ummar Kano na ci gaba da fargabar abin da ka iya faruwa idan duka sarakunan biyu suka ci gaba da shirinsu na gudanar da hawan salla.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Aminu Ado Bayero Fargaba gwamna hawan salla Rikicin Masarauta Ruɗani gudanar da hawan salla a gudanar da

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu

A jiya Asabar ce aka gudanar da taron farkawar musulmi wanda aka saba gudanarwa a ko wace shekara don tattauna al-amuran kawancen kasashe masu gwagwarmaya da kuma kasashen musulmi a yankin da kuma sauran kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa taron wanda aka gudanar a dakin taron shahida Muhammad Addurrah a nan Tehran ya sami halattar baki daga cikin gida da kuma kasashen waje.

Bakin dai sun hada da Nasser Abu Sharid wikilin kungiyar Jihadul Islami a nan Tehran,

Mohammad Hassan Akhtari, shugaban kwamitin kwamitin goyon bayan juyin juya hali a kasar Falasdinu. Mehdi Shoushtari daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran. Da kuma wasu daga baki daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran.

Nasser Abu Sharif wakilin Jihadul Islami, a Tehran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tsamar da HKI daga wargajewa tare da yarjeniyar da ya gabata. Yace falasdinawa sun amince da yarjeniyar, amma gwagwarmaya bata kare ba matukar HKI tana nan. Kuma tana ci gaba da kasha Falasdinawa a Gaza da yamma da kogin Jordan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter  A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
  • An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu
  • An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
  • Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano
  • CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya