Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu
Published: 13th, March 2025 GMT
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano.
Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar.
Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan KebbiYa ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku.
“Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da ƙiyasin kadarorin da jami’an kashe gobara na jihar suka ceto sun kai N180,318,000.
“Rayukan mutane bakwai ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi yayin da kuma aka ceto rayukan mutum bakwai.”
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kula da wuta cikin kulawa domin gujewa afkuwar gobara yayin da aka shawarci masu ababen hawa da su riƙa tuka mota cikin kulawa tare da bin dokar hanya musamman a lokacin da suke tafiya kan manyan hanyoyi domin guje wa haɗurran mota.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Kashe Gobara kashe gobara
এছাড়াও পড়ুন:
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku.
Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas.
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano SpalletiSauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da sauran laifukan sata a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke Kolawole, inda ta ce an kama shi da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan jami’ai sun lura da motsinsa da ya zama abin zargi.
Adebisi ta ce an same shi da tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano daga wani fashi da ya aikata a Opebi, inda ake zargin ya saci ₦200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da ke barci.
“Bincike ya ƙara tabbatar da cewa ya riga ya sayi sabbin kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sata, waɗanda suma aka kwato su daga hannunsa,” in ji ta.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Juma’a, jami’an RRS sun kama Sodiq Isa da Adekanmbi Ganiu bisa zargin yunkurin satar wayoyin hannu daga hannun fasinjoji a sassa daban-daban na Legas.