2025-10-13@22:26:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2722
«Yamma mai hedikwata a»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu. Babban jami’in kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk ya tabbatar a ranar Juma’a cewa, batun mika fursunoni da gawarwakin yahudawan sahayoniyya cikin sa’o’i 72 lamari ne na nazari, ba tabbas ba, a halin da ake ciki yanzu.” Abu Marzouk ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta amince da shirin Amurka da aka gabatar “a bisa ka’ida,” yana mai cewa “aiwatar da shi yana bukatar tattaunawa.” Ya kuma lura da cewa dukkan bayanai da suka shafi rundunar wanzar da zaman lafiya “yana bukatar fahimtar juna da fayyace shi dalla-dalla.” Dangane da batun makamai kuwa, Abu Marzouk ya bayyana a...
’Yan bindiga sun sace wata matar aure da ’ya’yanta biyu a yankin Bareke-Egbe a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan wani manomi mai suna Tokpe Gody da misalin karfe 2 na dare ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa biyu. Rahotanni sun ce Gody ya sha da ƙyar amma ya samu raunukan harbin bindiga a jiki da ƙafafuwansa, kuma yana karɓar magani a asibitin Egbe, inda likitoci ke cewa yana cikin mummunan yanayi. Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Adeyemi ya ce: “Tokpe Gody manomi ne mai fama da yadda zai ciyar da iyalinsa. Ya tsira da ƙyar daga ’yan bindigar, amma matarsa da ’ya’yansa...
“Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin gadar, sai sun biya ma’aikata su tura motarsu kafin su iya tsallaka rafi kana su ci gaba da tafiya. Rushewar Gadar Namne Ta Taraba Ta Tsayar Da Zirga-Zirga A Jihar Taraba kuwa, Gadar Namne dake kan hanyar Jalingo–Wukari ta rushe a watan Agustan 2024 bayan ruwan sama mai yawa, kuma har yanzu shekara guda bayan haka, babu wani gyara da gwamnatin tarayya ko ta jiha...
’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya. Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025. Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu Wani mazaunin yankin...
An gudanar da wani samame na musamman wanda ya kai ga gano bindigar da kuma cafke wadanda ake zargin. Jami’in da ya jikkata yana karbar magani a halin yanzu.” “A Damaturu, jami’an sashen A’ na Hedkwatar ‘Yansanda sun cafke Ibrahim Alhaji Ahmadu, mai shekaru 24, bisa zargin shiga gona da dabbobi da kuma yi wa wani manomi barazana da bindiga. An kwato bindiga mai kananan harsasai daga hannunsa. Rundunar ta jaddada cewa mallaka da amfani da makamai wajen tsoratar da fararen hula babban laifi ne.” Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa, “A Potiskum, an kama Dahiru Ali, mai shekaru 19, bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara uku. Bincike ya gano cewa wanda ake zargin ya taba aikata irin...
Anyanwu a cikin wasikarsa ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye wasu tsare-tsare don gudanar da taron, kuma za a gudana da shi kamar yadda aka tsara. “Muna tabbatar wa hukumar zabe cewa za mu gudanar da taron kamar yadda aka tsara tun farko ba tare da dagawa ba. “Ya kamata hukumar zabe ta yi watsi da wasikar da shugaban jam’iyyar ya tura mata tun da farko na dage toron,” ya aika wa INEC wasikar ne a ranar 26 ga Satumba ba tare da sa hannunna ba. A cewar sakataren, bai kamata INEC ta yi aiki kan wata wasikar da ba sanya hannunsa hade da na Damagum ba. Wata majiyar ta bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu ya nuna...
Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe A jawabinta, uwargidan shugaban Ƙasar ta ce wannan asibiti na nuna sakamakon jagoranci irin na hangen nesa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ta ce, asibitin zai ƙara inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Gombe da ma maƙwabtan jihohi, tare da...
Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau. “Babban kyawun demokuradiyya shi ne, ‘yancin samun damar kada kuri’a, duk wadanda ake zalunta; musamman mutanenmu a halin da ake ciki yanzu, za su samu damar kawar da wannan azzalumar gwamnati a zabe mai zuwa. Babu shakka, wannan shi ne ikon da babu wani dan takara da zai iya kwacewa daga al’umma,” in ji shi. Atiku ya kara da cewa, a shekara 65; Nijeriya ta kasance kasa wadda...
Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kaddamar da wasu sabbin motocin alfarma masu kujeru 18 guda 50, domin inganta ayyukan zirga-zirgar jama’a na jihar. Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya bayyana ci gaban a matsayin wani sabon babi a tarihin sufuri na Zamfara. A cewar Gwamnan, motocin bas din suna da kayan kariya na zamani da na jin dadi, wadanda suka hada da na’urorin sanyaya waje da sauran kayyakin jin dadin matafiya. Dokta Lawal ya bayyana cewa, da gangan aka samu jinkirin tura motocin bas din bayan isowarsu, inda ya ce gwamnati ta fara samar da tsare-tsare na sa ido da kuma bin diddigi don...
Ƴan ƙasar Congo sun fara mayar da martani kan hukuncin kisa da Babbar Kotun Sojin Ƙasar ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila ranar Talata a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa. Joseph Kabila mai shekaru 54, ya mulki jamhuriyar Demokradiyar Congo tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019 lokacin da ya mika mulki ga shugaba Felix Tshisekedi da ya gaje shi. Baya nan cikin kotu, lokacin yanke hukucin a ranar 30 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki, saboda yana can makwabciyarsu Rwanda inda yake zaman gudun hijirar siyasa shekaru biyu da suka gabata. Yayinda magoya bayan shugaba Tshisekedi ke yabawa matakin, wasu masana siyasa da ƴan adawa na kira da a yi taka-tsan-tsan. Jam’iyyar PPRD...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
Lamidon Akko da ke jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya nada Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu, sarautar Sarauniyar Yaki a masarautar. Basaraken dai ya karrama uwargidan shugaban ƙasar ce a ranar Alhamis a wani biki na musamman da ya gudana a fadarsa. An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku A cewar basaraken, ya ba ta sarautar ce domin yabawa da gudummawar da take bayarwa wajen kare marasa ƙarfi tare da tallafawa mata da yara a fadin ƙasar nan A yayin ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar Gombe, Remi Tinubu ta kuma ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative Flow With Confidence, wani muhimmin shiri na...
Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.” Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata. Yayin da yake jawabi a bikin da...
Jami’ar Tianjin wadda aka kafa a shekarar 1895 a matsayin jami’ar Peiyang, ita ce jami’ar zamani ta farko ta kasar Sin kuma ta yi na’am tare da amsa sunanta na yanzu ne a shekarar 1951. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani da ‘Akuskura.’ Ko wanne buhu na dauke da kwalabe 350, adadinsu ya kai kwalabe 2,450, wanda kudinsu ya kai ₦2,450,000. SP Kiyawa ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro, “Rundunar ta mika wadanda aka cafken da kayayyakin su da darajarsu ta kai N120,000,000 ga hukumar NDLEA, ta jihar Kano, domin ci gaba da bincike.” Hakazalika, jami’an rundunar sun kama wasu fitattun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja. Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello. Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM). Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata. “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa. Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su. ...

‘Yan siyasa a Nijar sun nemi da su yi aiki tare domin tabbatar da ba a samu cikas a zaben kananan hukumomi ba
An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe. Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa. Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna. Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa. Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja. Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu. Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa. Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda. Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar marigayin. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya ce Julius Ishaya, mutum ne nagari mai basira da jajircewa. Hakazalika, ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar, musamman kafin kafa gwamnatinsa. Ya ce a lokacin da Ishaya yake Kwamishinan...
Aƙalla mutum huɗu suka rasu yayin da aka sace wasu tara a wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Magama; ciki har da garin Ibeto a Jihar Neja. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mutum huɗu aka kashe, an jikkata wasu 11, sannan an yi garkuwa da mutum tara. Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Daga cikin waɗanda aka sace har da wanda ya wallafa rubutu a Facebook kan hare-haren ’yan bindiga a yankin, Barista Isyaku Muhammad Danjuma. Rahotanni sun nuna cewa wasu masu bai wa ’yan bindiga bayanai ne suka sanar da...
Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa na sojojin kasar da kuma na rundunar IRGC a lardin Hurmuzgan. Musawi ya ganewa idanunsa makamai na kariya da kuma na kai hare-hare kan makiya wadanda rundunonin ruwa a bangarorin biyu suke da shi da kuma lafiyar sojojin, inda ya bayyana amincewar sa da shirye-shiryen nasu. Musawi ya kara da cewa daga karshen kallafeffen yakin kwanaki 12 wanda HKI da kuma Amurka suka dorawa kasar...
Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, duk tare da wadannan hattsurran. Labarin ya kara da cewa, jirgin Alman, ya gamu da hare-hare daga yahudawan wanda ya tilasta masa jada baya zuwa wani waje. Banda ya an yanke dukkan kafafen sadarwa da waje. Gwamnatin yahudawan dai sun sha alwashin hana dukkan jiragen Ustura isa gaza, kuma ta bayyana cewa ta tura jiragen ruwan yaki, wadanda suka kama dukka mutanen da suke cikin...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka gudanar a jihar. A bisa al’ada dai Gwamna kan jagoranci hukumomin tsaro wajen gudanar da faretin bikin ranar a duk ranar daya ga watan Oktoba. To sai dai a bana, ba a ga Kwamishinan ’Yan Sandan na Kano ba, sannan babu ko dan sanda daya a wajen bikin. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi shahada a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba, 2024, a wani hari da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a yankin Dahiyeh da ke kudancin birnin Beirut. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Pars Today cewa, Shahid Hasan Nasrallah ya jagoranci kungiyar Hizbullah tun a farkon shekarun 1990, kuma...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.” Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun na Kassam sun watsa sanarwar a shafinsa na “Telegram’ da a ciki ya kunshi cewa, sun kai hare-haren ne akan ‘yan mamaya a kusa asibitin Jordan da kudancin unguwar “Tal Hawa” a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma rundunar ta Kassam ta ce ta kai wani harin akan motar soja da ta shiga cikin wata makaranta ta ” Rahibatul-Wurdiyyah” dake Tallul-Hawa.”. Har ila yau dakarun...
Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai linzami, ya kuwa shafi jirgin ruwan kai tsaye, yana kuma Shirin nutsewa. Kakakin sojojin Yemen din ya bayyana harin da cewa an kai shi ne saboda taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da yi wa kisan kiyashi. Haka nan kuma ya ce za su ci gaba da kai hare-hare akan duk wani jirgin ruwa wanda ya yi kokarin zuwa HKI ta hanyoyin ruwan tekun “Red-Sea”...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa. Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar...
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda game da rahoton ci gaban Sin na 2025 da cibiyar nazarin samar da ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, Guo ya ce ci gaban Sin mai inganci ya samar da damammaki ga duniya. Dangane da furucin Amurka na cewa za ta kara haraji kan katako, da kayan da ake sarrafawa daga gare shi, da ake shigarwa kasar daga ketare, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ba za a samu nasara a yakin ciniki da yakin haraji ba, kuma babu wata hanya ta fita daga ra’ayin ba da kariya ga kasuwa. Game da shawarar da Amurka ta gabatar...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da aka kakaba mata zuwa ga damammaki da bunkasa ci gabanta. Ya yi bayanin cewa: “Yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahayoniyya da Amurka suka kakaba wa Iran, wani gwaji ne kan karfin kimiyya da fasaharta. Ya ce: Iran ta fi karfi tare da mai da hankali a bangarorin kimiyya da fasaha.” Arif ya jaddada cewa: Al’ummar Iran suna bin tafarkin shahidai da kuma ci gaba da...

Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500 kan haramtacciyar kasar Isra’ila a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. Ya tabbatar da cewa: An yi nasarar kashe matukan jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila akalla 16 a daya daga cikin hare-haren makamai masu linzami da aka kai kan cibiyar horar da matukan jirgi. Wannan ya zo ne a cikin jawabin da Manjo Janar Yahya Rahim Safavi ya...
Ambaliyar ruwa a Sudan na barazana ga rayuwar dubban mutane tare da kara munana matsalolin jin kai Kogin Nilu ya mamaye yankuna da dama a Sudan, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubban mutane. Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da kadarori a jihar Al-Jazirah da kewaye, lamarin da ya shafi dubban iyalai tare da barin su cikin bukatar tallafin gaggawa da matsuguni da abinci da magunguna. Haka zalika ruwan sama kamar da bakin kwarya ya dakatar da zirga-zirgar wasu jama’a a wasu yankuna, yayin hukumomin cikin gida suke kokarin rage barnar da ake amma lamarin ya foi karfinsu sakamakon karancin kayan aiki. Ambaliyar ruwan ta kara ta’azzara matsalar jin kai a birnin El Fasher da sauran garuruwa, inda mazauna garin...
“Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho dake ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” in ji Daraktan PTAD. Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi da walwalar masu karɓar fanshon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa duk da tana maraba da tsayawa takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Zaɓen 2027, amma ya kwana da sanin cewa har yanzu ’yan ƙasar ba su mance da badaƙalar da aka tafka a lokacin gwamnatinsa ba. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar da yammacin ranar Litinin, ta ce ’yan Najeriya na sane da “rashin takaɓus” a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya. Jama’ar gari sun kama ’yan bindiga 3 a Kastina An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar mai taken “Muna maraba da tsohon shugaban ƙasa zuwa takarar shugabancin ƙasa”, “amma ’yan Najeriya na sane...
A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti. Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku. Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro da mafarauta don bin sahun ‘yan bindigar, da nufin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke masu laifin. A wani samame daban, Abiodun ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan tare da mafarauta sun kai farmaki wani dajin da ake zargin maɓoyar masu garkuwa, a cikin dajin Kokolo da ke Ƙaramar Hukumar Magama. A lokacin arangamar da aka yi da ‘yan bindigar, an...
Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba ba zai rage darajar wannan muhimmiyar rana ta tarihi ba,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na ba da haƙuri kan wannan sauyi, amma sauran ayyukan da aka tsara domin zagayowar ranar za su ci gaba kamar yadda aka tsara. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa, bukukuwan al’adu, da wasu abubuwa da aka shirya.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau 29 ga wata, an gudanar da bikin karfafa hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na Sin wato CMG, da mabambantan bangarori na yankin Hong Kong. Jagoran yankin musamman na Hong Kong John Lee Ka-chiu ya bayyana cewa, idan aka waiwayi tarihi, gwamnatin Hong Kong da CMG sun kasance suna hadin gwiwa sosai da juna. Sun yi hadin gwiwa da juna a fannonin ba da rahotannin manyan bukukuwa, da fadakar da al’ummu manufofi masu muhimmanci, da daidaita al’amura na gaggawa. Bikin karfafa hadin gwiwa na yau ya alamanta sabon babin hadin gwiwar CMG da al’ummar Hong Kong. Jerin matakan da aka dauka, ba ma kawai sun dace da manufofin kasa ba, sun kuma amsa bukatun al’ummar Hong...
A wata hira da gidan talabijin din Aljazeera yayi da sakataren cibiyar kula da yan gudun hijira a kasar Nowy ya fadi cewa babban abin da yake damunsu shi ne inda duniya ta yi shiru kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda israa’ila ke kisan kiyashi. Dubban daruruwan alummar Gaza ne suka tarwatse da suke fuskantar tsananin bala’I kamar jan Egeland yadda ya bayyana, yace dole ne a a dakatar da kisan kiyashin da isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza, Haka zalika ya nuna damuwar sosai game da gum da baki da majalisar dinkin duniya ta yi akan batun gaza, babban abin da muwar shi ne yadda duniya take nuna halin ko in kula da abin da...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD. A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun damar shiga ko samun hutu daga aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba tare da kiyaye sharaɗin da NERD ta shar’anta ba. Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu A ƙarƙashin sabon tsarin wanda zai soma aiki daga 6 ga watan Oktoba, NERD ta wajabta cewa a yanzu rajistar ɓautar ƙasa tana ta’allaƙa ne da miƙa aikin binciken...
Da yammacin yau Litinin ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taron nazari karo na 22, kan yadda za a sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar. Yayin da ya jagoranci taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, “Ya kamata mu tattara, da kuma amfani da darussan tarihi, mu mayar da hankali kan hakikanin ayyukan addinai na kasa, da sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar, da kuma jagorantar addinai don daidaita al’umma mai ra’ayin gurguzu”. Xi Jinping ya kara da cewa, ana bukatar sa kaimi ga dunkulewar addinan kasar Sin, tare da kyawawan al’adun gargajiya na kasar bisa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano. Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa a gaban kuliya. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundumar ta kuma kama kwayoyin Tramadol da kudinta ya kai Naira miliyan 60.3 da kwayar Pregabalin ta Naira miliyan 22.4 da kuma sinki 523 na tabar wiwi da injinan tura kudi na POS guda biyar daga hannun wadanda ake zargi a sassan jihar. Kwamishinan ya ci gaba da cewa rundunar ta kama...
Shigowar Ganduje Da Sauya Mallaka A Asirce Sakamakon barazanar soke yarjejeniyar ya sa dole wanda ya kafa kamfanin, Ahmad Rabiu, ya nemi sabon abokin tarayya. A cikin wannan lokacin ne, a ranar 5 ga Maris, 2020, aka gudanar da wani taro na musamman na kamfanin Dala Inland Dry Port. A cikin wannan taron, an cire duk tsoffin daraktocin kamfanin, an kuma naɗa ƴaƴan Ganduje uku da wani ɗan nasa na kut da kut mai suna Abubakar Bawuro, a matsayin sabbin daraktoci. An ba kowane ɗaya daga cikin ƴaƴan Ganduje hannun jari na kashi 20% kowanne, haka kuma aka ba Bawuro da Rabiu kashi 20% kowanne. Wannan shi ne lokacin da aka cire Jihar Kano gaba ɗaya daga cikin masu mallakar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa bukatun gwamnatin Amurka daga kasar Iran ba abar amincewa ba ne. Shugabany a bayyana haka ne a ranar Asabar kafin ya bar birnin Newyork zuwa Tehran bayan ya halarci taron babban zauren MDD na shekara shekara. Yace: Bamu daidaita da su kan snapback ba, sai Amurka tace mu mika mata dukkan makamashin Uranium da muka tashe, su kuma zasu bamu damar watannin uku kacal na Rashin takunkuman tattalin arziki, sannan su sake dawo da su. Shugaban yace wannan ba zai taba yiyuwa ba. Ya ce kasashen turai sun zama mabiyan Amurka kawai, ba zasu iya yin wabu batare da amincearta ba. Ya kuma kara da cewa mun cimma yarjeniya da kasashen turai,...
Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma Iran ba zata kiyayesu ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa kasashen Rasha da China wadanda suka kasance mambobi na din din din a kwamitin tsaro na MDD sun tabbatar da cewa abinda turawan suka yi baya bisa ka’ida. Ya ce idan wadannan kasashe da Amurka suka dauke wani bataki kan Iran, iran zata maida martini mai tsanani a kansu. Qalibof ya bayyana cewa kasashen sun yi amfani da tattaunawa da a matsayin makami don cimma manufarsu da durkusarwa da...
LEADERSHIP ta labaro cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya rantsar da Hajiya Zainab Baban Takko a matsayin Kwamishina ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024 tare da wasu sabbin kwamishinoni biyu. Kafin ta hau kan wannan kujerar, ta zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Bauchi wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya naɗata a watan Yulin 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jiya Lahadi ne masu tafiyar da ayarin jiragen ruwan dake son keta killace Gaza ” Sumud” su ka sanar da cewa, tsakaninsu da yankin Gaza bai wuce kilo mita 825 Ba. Ayarin jiragen ruwan dai yana kunshe da kananan jiragen da sun kai 50, sun fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuki na HKI da hakan ya haddasa yankewar hanyoyin sadarwa,ba tare da an sami asarar rayuka ba. Mutanen da suke cikin jiragen ruwan sun hada masu fafutuka da su ka fito daga kasashe 45 na duniya. Daga kasar Malysia kadai da akwai mutane 500 sai Faransawa 54 da kuma ‘yan kasar Belgium 15 daga ciki har da ‘yan gwagwarmayar kare muhalli Greta Thunberg. Wani daga cikin masu fafutuka...
A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa; Manyan jami’an diplomasiyyar kasashen uku na turai sun yi wani taron sirri a birnin Moscow, inda su ka gargadi Rasha akan keta hurumin samaniyar kasashen mambobi,suna masu cewa za su iya kai wa jiragen Rashan hari. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” din ya ambato jami’an kasashen na turai da su ka halarci taron suna nakalto wannan gargadin, bisa cewa cikin ganganci ne jiragen na Rasha su...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 30 domin biyan buƙatun ’ya’yanta, ko kuma ta fuskanci yajin aiki. Wa’adin na ƙunshe ne a sanarwar Bayan taron ƙungiyar, ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman; Sakatare Janar, Dakta Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dakta Abdulmajid Ibrahim. Shugaban NARD, Dakta Suleiman, wanda aka zaɓa a taron domin maye gurbin Dakta Tope Osundara, ya ce wannan wa’adin ba a bayar da shi da wasa ba. “Ba za mu ci gaba da kallo mambobinmu suna aiki cikin yanayi marar tsaro yayin da aka yi watsi da walwalarsu ba. Idan ba a warware matsalolin cikin kwanaki 30 ba, za mu ɗauki mataki,” in ji...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Ɗangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan ƙwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Ɗangote ta salami ma’aikata fiye da 800. Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba, da an bi wasu hanyoyi. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Waɗannan hanyoyi shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai binciko. Domin sauke shirin, latsa nan
A yau Lahadi ne aka gudanar da biki mai taken “Bude sabon babi a sabon zamani: Bikin zurfafa hadin gwiwa tsakanin CMG da bangarori daban daban na Macao” a yankin Macao na kasar Sin. Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG Shen Haixiong, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa, Shen Haixiong ya ce “A yau CMG ya sake kaddamar da ayyukan hadin gwiwa da dama tare da bangarori daban daban na Macao, kamar gabatar da wani fim mai bayana labarai mai suna “Macao: Gidan adana kayayyakin tarihi a fili”, da kuma fitar da “Gadon ruhin kishin kasa: Hanyar yawon shakatawa ta wuraren tarihi dake nuna kishin kasa na Macao”, ta yadda...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka bayyana a matsayin haramtacciyar hanya sakamakon daukar matakin sake dawo da takunkuman da kasashen Turai uku suka yi kan Iran. Qalibaf ya yi bayanin cewa: Share fagen hanyar da za a bi wajen sake kakaba takunkuman da kasashen Turai uku suka yi da kuma mayar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran, ba bisa ka’ida ba ne, yana...
An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama. Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal. Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba. Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup...
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa kwale-kwalen a cikin nasu jirgin ruwa, sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 17. Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki Kwale-kwalen na wani kamfani ne da ke aikin jigilar fasinjoji tsakanin jihohin biyu a kan teku. A ‘yan shekarun baya matsalar satar mutane da garkuwa da su ta...
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa kwale-kwalen a cikin nasu jirgin ruwa, sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 17. Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki Kwale-kwalen na wani kamfani ne da ke aikin jigilar fasinjoji tsakanin jihohin biyu a kan teku. A ‘yan shekarun baya matsalar satar mutane da garkuwa da su ta...
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargin cewa, cikin watanni shida, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samu karin kaso daga gwamnatin tarayya fiye da yadda ya samu a cikin shekaru 8 da ya yi yana gwamna. Batun rabon kuɗaɗen wata-wata ga Jihohin dai ya zama abun muhawara a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano “A yau zan iya bugun ƙirjina kuma kowanne daga cikin gwamnonin nan zai iya tabbatar da cewa, rabon da ake bai wa jihohin ya ninka sau uku, kuma akwai l isassun kuɗaɗe daga ƙananan hukumomi.” in ji Ganduje Da yake...
Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kwanakin baya, shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel ya yi hira da wakilin rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, kasarsa ta Cuba ta yi nazari kan kwaskwarimar da kasar Sin ta yi, kamar su yadda kasar Sin ta mika iko ga kananan gwamnatocin kasar don sa kaimi ga daidaita harkokin sassan kasar, da daukar jerin matakai wajen yin kwaskwarima a kauyuka don tabbatar da wadatar abinci, da daidaita huldar dake tsakanin manyan tsare-tsare da mika iko ga kananan gwamnatoci, da kuma kasuwanci, da sa kaimi ga raya kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire, da bunkasa sha’anin al’adu da yawon bude ido a kasar don maida al’adu su zama jigon sha’anin yawon bude...
A jera kwakwamba, kifi, abocado, ko duk abin da kuka zaba. Kada ku cika sosai don kada ya warware. Sai Nadewa: Da taimakon tabarma, za a fara nadewa daga kasa sannan a yi sama. A matsa sosai yayin nadewa don ya daure sosai. Idan kuka kai karshen nori, ku dan shafa ruwa ko binegar a bakin domin ya likewa. Yankewa: Sannan a yanke cikin kanana da wuka mai kaifi. Ku jika wukar da ruwa kafin yankewa don kada ya manne. A Jika da miya: Sai a ci da miyar jajjagen da kukayi. Aci dadi lafiya. Shawara: Idan bakwa son kifi za ku iya amfani da nama da aka dafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...

Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani? Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala karatun jami’ansu da maki iri ɗaya a matakin Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a wannan shekarar daga jami’o’i daban-daban. Maryam Salisu da yayanta Suleiman Salisu kowannensu ya kammala karatun digirinsa na farko ne da maki 4.51 daga fannin Kimiyyar Kwamfuta, a wannan shekara ta 2025 a Jihar Katsina. A halin yanzu Suleiman ya fara aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) a yayin da ƙanwar tasa...
A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya. Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban. “Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki. Kwamishinan...
Gabanin shekarar 2005 da gwamnatin Kano ta hana sana’ar haya da babur saboda matsalar tsaro da ta kunno kai jihar, jigilar fasinjoji ta ta’allaƙa ne da motocin haya na hayis, ko tasi, a kuma farashi mai sauƙi. Sai dai sannu a hankali, waɗannan motocin hayar suna neman zama tarihi musamman a birane saboda zuwan babura masu ƙafa uku, waɗanda aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ a lunguna da saƙo. Wata ƙididdiga da Hukumar Samar da Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano ta fitar, na nuna gwamnatin jihar tana samun aƙalla Naira miliyan shida a kullum daga harajin Naira 100 da ta sanya wa masu sana’ar A Daidata Sahu — wanda a shekara ya kai Naira biliyan 2.1. Haka kuma...
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna nan a gidan yari kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci. Kwamishinan ’Yansandan Jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa kwazon da DPO da ’yan banga suka yi da gaggawa, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yansanda da al’umma wajen magance miyagun laifuka. Ya kuma tabbatar wa mazauna Jihar Kebbi cewa, rundunar ‘yansandan ta jajirce wajen kawar da masu aikata laifuka da samar da yanayi mai tsaro. Daga nan sai ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa. Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu...
MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen kamfanoni 11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a shekarun baya ne dai MDD ta fara fitar da sunayen kamfanonin da suke aiki tare da HKI a wajen keta dokokin kasa da kasa da keta hakkokin al’ummar Falasdinu. Daga cikin kamfanonin bayan nan da aka kara sunayensu da akwai Heidelberg na kasar Jamus da kuma Ineco na kasar Spain. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
Ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da su a kotu. ’Yansanda sun bayyana cewa kamen na cikin ƙoƙarin murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar Kaduna da kewaye. Sun ƙara da cewa waɗanda aka kama sun amsa laifukansu, ciki har da fashi, satar waya da kuma sayar da kayan sata. Kwamishinan ’Yansandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya jinjina wa jami’an saboda jajircewarsu wajen gudanar da aikin. Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka kuma, ya buƙaci ’yan kasa su kasance cikin shiri, tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama masu laifi. Ya ce, “Idan muka haɗa kai, za mu tabbatar Kaduna ta kasance...

A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri. Ya zuwa yanzu, Chen da Wang sun riga sun koma sashin gwaje-gwaje na Wentian lami lafiya, al’amarin da ya shaida babbar nasarar da suka samu wajen gudanar da ayyuka a wajen kumbon. Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun...
Wanda duk zai gaya maka gaskiya musamman wanda yake zaune ko ya ke zuwa wuraren da aka samu matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi na jihar Katsina zai fada maka cewar an samu zaman lafiya fiye da lokutan baya. An sha ruwaito wadanda wannan bala’i ya shafa suna maida martani ga masu suka sulhu da cewa duk wanda baya goyon bayan wannan sulhu dan ba a wannan yanki yake da zama ba. Sai dai kuma yin sulhu da barayin daji ba yana nufin an samu zaman lafiya dari-bisa-dari ba. Ana dai samun saukin kai hare-haren ‘yan bindigar amma ba wai an daina ba ne baki daya. To, ta ya ya al’umma za su amfana da wannan yarjejeniyar zaman sulhu da...
A ranar Litinin aka gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a Birnin Paris, inda ake karrama fitattun ’yan ƙwallon duniya. A bana, Ousmane Dembele na Ƙasar Faransa da PSG ne, ya lashe kyautar maza, yayin da Aitana Bonmati ta Spaniya ta lashe ta mata karo na uku a jere. An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Abin farin ciki ga Najeriya shi ne, mai tsaron ragar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta zo ta huɗu a jerin mata, wanda shi ne matsayi mafi girma da wata ’yar Najeriya ta taɓa samu. Ga jerin ’yan Najeriya da suka taɓa shiga cikin jerin waɗanda suka fafata neman kyautar Ballon d’Or:...
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin. ‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad Store’ Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata. Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin...
Magajin garin Landan ya caccaki shugaban Amurka Trump, yana mai cewa shi mai nuna wariyar al’umma ce tare da kyamar musulmi Magajin garin Landan Sadiq Khan ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai nuna wariyar al’umma kuma mai kyamar musulmi,” bayan da Trump ya zarge shi da neman aiwatar da shari’ar Musulunci a babban birnin Birtaniya. Khan ya shaida wa tashar Sky News cewa: “Yana ganin Trump a matsayin mai nuna wariyar al’umma, mai dabi’ar bunsuro, mai son zuciya, kuma mai kyamar musulmi.” Ya yi nuni da cewa, Landan ce ta farko a cikin alamomi da dama, kamar zuba hannun jari na kasashen waje, ya kuma jaddada cewa “yana matukar alfahari da cewa Landan ce birni mafi girma...

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari. Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas. Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru...
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo. Bikin da ba a taba yin irinsa a Ibadan ba Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Dattawa ’Yan asalin Ibadan (CCII), Cif Ajeniyi Ajewole ya ce, dukkan attajirai ’yan asalin Ibadan an dora masu haraji daga Naira miliyan 10 zuwa sama a matsayin gudunmawarsu ga wannan biki da aka fara da addu’ar rokon Allah a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce, “mun kammala shirin yin bukukuwan nada...
Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma wasu lamuran da suka shafi al’ada a fadin kasar, wanda ya kai kaso 15. Misali, yankin Arewa Maso Gabas, kacal irin wadannan hare-haren babu kakkautawa da mahara ke kai wa ya dakatar da yara miliyan biyu daga zuwa Makaranta inda hare-haren suka lalata gine-genen Makarantu da dama hakan kuma ya kara haifar da karancin Malaman. Malamai 915,913 kacal ne a matakin karatun Firamare ke koyar...
A Benuwe, sojoji sun kashe wani, sun kuma ceto fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka ceto wasu uku a Kwara. A Nasarawa, an kama mutane biyu da ke safarar miyagun ƙwayoyi, a Imo kuma, an cafke masu safarar bindigu. Hakazalika, a Anambra, sojoji sun daƙile ayyukan IPOB/ESN tare da ƙwato abubuwan fashewa. A jihohin Delta da Bayelsa kuma, an ƙwato bindigogi, harsasai da miyagun ƙwayoyi da yawa. Sama da lita 1,200 na man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, ak kama a Ribas da Bayelsa. Gaba ɗaya, sojojin sun ƙwato bindigogi, harsasai, abubuwan fashewa, babura, man fetur, takin zamani da miyagun ƙwayoyi daga hannun ‘yan ta’adda da sauran masu laifi. Daga kanmu,...
Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United. Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya. Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029. Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da babban tsarin ban ruwa a wurin, har ya mai da sassan hamada su zama gonaki. A cikin hamadar da ke gundumar Qiemo, ana ta kara samun dausayi, inda masarar da malam Li Wenbin ya shuka ta kusan nuna. A cikin shekaru goma da suka gabata, karuwar gonaki a jihar Xinjiang ta kai fiye da muraba’in kilomita 8000, wanda ya sa jihar zamanto yankin da ya...
Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci. Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi. Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa. A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan...
Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 na kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kai, a babban zauren taron jama’a na Xinjiang. Kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin. Memba dindindin na ofishin siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ko CPPCC, kuma shugaban tawagar kwamitin kolin jam’iyyar Wang Huning, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Kazalika, memba dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Cai Qi shi ma ya halarci taron. A cikin jawabinsa, Wang Huning ya bayyana cewa, kwamitin kolin JKS a karkashin jagorancin Xi Jinping, ya ci gaba da dubawa, da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓar Naira miliyan biyu a hannun wani mutum, sannan suka harbe shi saboda kuɗin ba su kai adadin da suke nema ba. Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka mai shekaru 25, Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma. Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas Sun harbi mutumin a ƙafa bayan sun gano ba shi da kuɗi sosai a asusun bankinsa. Kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce sun samu kiran gaggawa cewa an yi garkuwa da wani mutum a gidansa da ke Ogwashi-Uku. ’Yan sanda sun bi sahun...