Aminiya:
2025-11-27@21:55:08 GMT

Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji

Published: 8th, October 2025 GMT

Tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya ce bai yi murabus daga muƙaminsa ba saboda yana da laifi.

Nnaji, ya yi murabus ne a ranar Talata bayan cece-ku-ce ya karaɗe kafafen watsa labarai tambaya kan sahihancin takardun karatunsa.

Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki

Rahoton da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa ya nuna cewa Jami’ar Nsukka (UNN), ta ƙaryata bai wa Nnaji takardar shaidar kammala digir a jami’ar.

Jami’ar ta ce Nnaji ya fara karatu a makarantar a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi shaidar kammala digiri ba.

Sai dai a wata sanarwa da Nnaji ya fitar da kansa, ya ce sun ɓata masa suna da shafe tsawon shekaru ya karewa ta hanyar aiki tuƙuru da gaskiya.

Ya ce: “Bayan tunani mai zurfi da shawara da iyalina da abokaina suka ba ni, na yanke shawarar yin murabus daga muƙamina na Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha.

“Wannan hukunci ba don na aikata laifi ba ne, face saboda ina son kare martabar ma’aikatar da kuma barin shari’a ta bi tafarkin da ya dace.”

Nnaji, ya ƙara da cewa an yi amfani da siyasa wajen ɓata masa suna ta hanyar yaɗa ƙarya.

“Waɗannan ƙarairayi sun min ciwo, sun sanya cikin damuwa, kuma sun fara zama cikas ga ayyukan ma’aikatar da kuma shirin ‘Renewed Hope’ na Shugaba Tinubu,” in ji shi.

Ya jaddada cewa ya yi murabus ne saboda kare ƙa’idar aiki da mutunci, ba saboda yana da laifi ba, inda ya tabbatar da cewa gaskiya za ta yi halinta.

Nnaji, ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, saboda ba shi damar yin aiki a gwamnatinsa, kuma ya ce zai ci gaba da goyon bayan shugaban wajen gina Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Murabus Takardar Bogi zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata.  Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar  Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik.

A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan dangantaka mai tsawo da ke tsakanin Iran da Pakisatan, da kuma bukatar a kara zurfafata.

Sharif a nasa bangaren ya bayyana cewa nan ba da dadewa waministan harkokin wajen kasar Mohammad Ishak Dar zai ziyarci Tehran inda ake saran zai rattaba hannu kan yarjeniyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, daga ciki har da batun kammala aikin shimfida bututun gas  daga kasar Iran zuwa Pakistan. Da kuma harkokin sadarwa.

A cikin wannan shekarar ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyar bunkasa kasuwanci ta dalar Amurka billion 10 a tsakaninsu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu.
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina