Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC
Published: 8th, October 2025 GMT
Shirye-shiryen sun kammala domin Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara goma a ranar Talata.
Kafin Yakubu ya sauka daga mukaminsa, rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na nazarin mutum uku da ake has ashen za su iya maye gurbinsa: Farfesa Joash Ojo Amupitan, Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da Farfesa Lai Olurode.
Wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa Aminiya cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen don maye gurbin tsohon shugaban INEC.
Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC daga hannun Shugaban ƙasa — IPACFarfesa Yakubu ya sauka daga mukaminsa bayan ganawa da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche-Mbu, wata kwamishiniya a hukumar, wadda ta karɓi mukamin a matsayin shugabar rikon kwarya.
Aminiya ta gano cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da sunan wanda ya zaɓa a matsayin sabon shugaban INEC ga mambobin Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa a taron da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis.
Ana sa ran za a sanar da sunan sabon shugaban INEC bayan taron.
Matukar ba a sami sauyin shawara ba, Farfesa Amupitan, wanda lauya ne mukamin SAN, na iya zama wanda zai dare kan shugabancin hukumar.
Amupitan
Yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (bangaren gudanarwa).
An haife shi a ranar 25 ga Afrilu, 1967 a Aiyetoro-Gbede, Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.
Farfesa ne a fannin Shari’a, musamman a dokar shaida, kuma ya shafe shekaru da dama yana koyarwa a jami’a.
Da aka tuntubi Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ƙi yin tsokaci kan jita-jitar cewa Farfesa daga jihar na iya zama shugaban INEC.
Ya ce: “Gwamnati ba ta yin tsokaci a kan jita-jita.”
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Timothy Golu, wanda ya ce ya san Amupitan fiye da shekaru goma, ya bayyana shi a matsayin malami abin girmamawa kuma gogaggen ma’aikaci.
“Lokacin da nake ɗalibi a Jami’ar Jos, Amupitan na daga cikin malamai da ɗalibai ke iya kai ƙara gare su a kowane lokaci. Don haka, ba ni da shakku cewa zai gudanar da aikin cikin gaskiya idan har ana duba shi,” in ji Golu.
Farfesa Amupitan ya rike mukamai da dama na ilimi da gudanarwa, ciki har da wakilin tsangayar Shari’a a kwamitoci da dama a Jami’ar Jos; Shugaban Sashen Dokar Jama’a; Shugaban Tsangayar Shari’a; Mamba a Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jos da Majalisar Gudanarwa ta Cibiyar Nazarin Shari’a ta Ƙasa da Majalisar Ilimin Shari’a da sauransu.
Mamba ne a ƙungiyoyi da dama na ƙwararru ciki har da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya (NIM) da Ƙungiyar Malaman Shari’a ta Ƙasa.
Binciken Farfesa Amupitan ya shafi fannoni da dama ciki har da samar da tsarin doka don keɓance harkokin gwamnati, gyaran dokokin zaɓe, da dokar masana’antar man fetur a Najeriya.
Ya wallafa fiye da makaloli 50 da suka haɗa da mujallu, babin littattafai, taruka, nazari, da rahotannin bincike, kuma ya taka rawa a aiwatar da ayyuka na ƙasa da na ƙasashen waje.
Liman
Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman tsohon alkalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ne.
An haife shi a shekarar 1959, ya zama lauya a 1984, kuma dan asalin jihar Nasarawa ne. Ya shafe fiye da shekaru 25 yana aiki a matsayin alkalin kotu.
Ya shahara da shari’o’i masu tasiri ciki har da hukuncinsa da ya dakatar da dawo da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano, da kuma dakatar da matakin kama tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.
Lai Olurode
Farfesa Lai Olurode masanin zamantakewa ne, malami kuma ɗalibi mai daraja ta farko a fannin nazarin halayyar dan-Adam daga Jami’ar Legas (UNILAG), Akoka.
Ya kuma yi karatun Shari’a a UNILAG inda ya samu digiri na LL.B a 1990, kuma ya zama cikakken lauya shi a 1991.
Ya fara koyarwa a UNILAG tun 1980, ya zama Farfesa a 2000, ya rike mukaman Shugaban Sashi da shugaban Tsangayar Nazarin dan-Adam.
Ya shafe fiye da shekaru 40 yana koyarwa kafin ya yi ritaya, kuma aka naɗa shi Kwamishina ta Ƙasa a INEC a ranar 30 ga Yuni, 2010, inda ya kula da jihohin Oyo, Ogun da Ekiti.
Aminiya ta ƙara gano cewa Yakubu ya riga ya shirya komai na sauka daga mukaminsa, ya rubuta bayanin mika mulki, yana jiran izini kawai.
Wata majiya a hukumar ta shaida wa wakilinmu cewa Yakubu ya kammala duk shirye-shiryen zaɓen Anambra, kuma saukarsa ba za ta shafi gudanar da zaɓen ba.
“Akwai abubuwa 13 da ke cikin tsarin, Yakubu ya kammala 11, saura biyu: ƙarshen yaƙin neman zaɓe da zaɓen da kansa,” in ji majiyar.
Da aka tuntubi tsohon Daraktan INEC, Nick Dazang, ya ce da zarar Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta zauna ranar Alhamis, “yana nufin za mu iya sanin wanda zai gaje shi kafin mako mai zuwa. Ban yi zaton saukarsa za ta shafi aikin hukumar ba.”
Shugaban INEC mafi tsawon wa’adi
Farfesa Yakubu shi ne shugaban INEC ɗaya tilo da ya yi wa’adi sau biyu na tsawon shekaru goma.
Shi ne shugaban INEC na uku da ya kammala wa’adin aikinsa, yayin da mafi yawan waɗanda suka gabace shi suka sauka daga mukami sakamakon cece-kuce ko kuma sauyin gwamnatin da ta naɗa su.
Najeriya ta taɓa samun hukumomin zaɓe guda shida daban-daban, tare da shugabanni 14 da ɗaya a matsayin na rikon kwarya.
Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya gaji Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban INEC a shekarar 2015, shi ne na farko da aka sake naɗa wa wa’adi na biyu, lamarin da ya sa ya zama shugaban da ya fi kowane tsawon wa’adi a tarihin hukumar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mahmud Yakubu Farfesa Amupitan ciki har da Jami ar Jos
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar.
Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta.
Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako.
Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista da kungiyar domin kasacewa a karkashin inuwa daya ta yadda za su ci moriyar tanade tanaden ta, sannan su kasance masu mutunta shugabanci da kuma bin doka da oda domin inganta rayuwar su.
Ya ce yayin da kungiyar ta ke da ‘yan dako kimanin dubu 20 a karkashin ta, akwai bukatar duk ‘yan dakon da ba su da katin zabe su karbi sabo ko kuma su sabunta wanda ya bata ko ya lalace domin amfani da damar su wajen zaben shugabanni.
A sakon sa, Hakimin Maigatari Alhaji Sani Alhassan Muhammad wanda ya sami wakilcin Sarkin Kasuwar Maigatari Alhaji Muhammadu Sarkin Kasuwa, ya bukaci sabon sakataren kungiyar Malam Muhammad Tajudeen ya kasance mai nuna gaskiya da adalci wajen huldar sa da ‘yan dako da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci, inda ya bayyana murnar samun wannan mukamin.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin hatsin Maigatari, Malam Mu’azu Bako da Shugaban leburorin Dingas na Jamhuriyar Nijar Malam Lawwali Hassan.
Usman Mohammed Zaria