Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran
Published: 12th, September 2025 GMT
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a daren jiya Alhamis da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, inda suka mai da hankali kan shirin nukiliyar Iran da batutuwan da suka shafin yankin.
tattaunawar na zuwa ne bayan da Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka cimma matsaya ta hadin gwiwa a nan gaba.
Tehran ta dage kan kare hakkinta a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), yayin da ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki wani mataki mai karfi kan ayyukan sojan Isra’ila a yankin.
Manyan kasashen yammacin duniya sun yi barazanar maido da takunkuman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka dage a baya, lamarin da ke kara nuna fargabar sake samun koma-bayan diflomasiyya.
Tattaunawar ta jaddada kokarin Tehran na kare hakkinta na nukiliya yayin da take mayar da martani kan hare-haren soji da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin.
Araghchi, Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya da su yi Allah wadai da “hare-hare ” kan cibiyoyin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Araghchi ya soki E3 (Birtaniya, Faransa, Jamus) saboda yin watsi da ta’addancin Amurka da Isra’ila yayin da yake barazanar farfado da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
A nasa bangare sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da IAEA a baya-bayan nan, yana mai jaddada goyon bayan MDD ga ci gaba da tattaunawa da diflomasiyya kan batun nukiliyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa September 12, 2025 Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran September 12, 2025 Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar September 11, 2025 Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu September 11, 2025 Qatar Ta Bukaci A Gurfanar Da Netanyahu A Gaban Kuliya Don Fuskantar Adalci September 11, 2025 Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
Dan kasar Iran Aryan Salawati ya sami kyautar tagulla a wurin gasar kirkire-kirkire ta kasa da kasa wacce aka yi a kasar China.
A yayin wannan bikin dai masu kirkira daga kasashe masu yawa ne su ka gabatar da abubuwan da su ka kirkira.
Matashin dan kasar Iran ya kirkiri karamar na’ura wacce take iya auna yanayi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci