An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi
Published: 13th, August 2025 GMT
Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dr) Rilwanu Suleiman Adamu, ya naɗa tsohon babban jami’in Hukumar Kwastam mai ritaya, Alhaji Bala Muhammad Gidado, a matsayin Sarkin Alkaleri, wanda zai gaji marigayi Sarkin Alkaleri, Alhaji Muhammad Abdulkadir.
Da yake jawabi yayin naɗin, Sarkin Bauchi ya jaddada cewa sabon Sarkin Alkaleri ya samu wannan muƙami ne bisa la’akari da cancanta, ilimi, gogewa da kuma nagarta.
Ya buƙaci sabon sarkin da ya yi amfani da wannan gogewa wajen ci gaban masarauta, tare da tabbatar da gaskiya, adalci, riƙon amana da haɗin kan jama’a.
Sarkin ya yi addu’ar Allah Ya ƙara zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Bauchi, tare da yaba wa Gwamna Bala Abdulqadir Muhammad, bisa ayyukan raya ƙasa da inganta tsaro.
A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Alkaleri, Garba Hassan Bajama, ya gode wa Sarkin Bauchi bisa tabbatar da wannan sarauta, yana mai alƙawarta haɗin kai tsakanin gwamnati da masu sarauta wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Bikin naɗin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, masu riƙe da muƙaman gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki, lamarin da ya nuna muhimmancin mukamin Sarkin Alkaleri a tsarin masarautar Bauchi.
Bayan naɗin, an sanya wa sabon sarki rawani da alkyabba a fadar Sarkin Bauchi, sannan jama’a suka raka shi cikin waƙe-waƙe da kaɗe-kaɗe na farin ciki zuwa garin Alkaleri.
Sabon Sarkin ya isa fadarsa a kan doki, inda aka gudanar da hawan durbar na murnar karɓar sarautar, tare da miƙa masa wuƙa, takobi da Alƙur’ani a matsayin alamar mulki.
Alhaji Bala Muhammad Gidado, wanda ya yi ritaya daga Hukumar Kwastam, yanzu shi ne Sarkin Alkaleri na tara a tarihin masarautar Bauchi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rilwanu Suleiman Adamu Sarkin Alkaleri Sarkin Bauchi Sarkin Alkaleri Sarkin Bauchi sabon Sarkin
এছাড়াও পড়ুন:
Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp