2025-05-15@18:10:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4537

«shugaban hukumar»:

    Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune. “Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron daji a faɗin ƙasar nan domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a cikin dazukan Najeriya. A ƙarƙashin wannan sabon shiri, za a ɗauki sama da mutane 130,000 aiki da za su samu horo na musamman da kayan yaƙi na zamani domin kare dazuka guda 1,129 da ke sassa daban-daban na ƙasar nan. Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya fitar a shafinsa na X. Sanarwar ta bayyana cewa an...
    Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Rano/Bunkure/Kibiya, sun sauya sheƙa a ranar Alhamis. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Hakazalika mamba mai wakiltar mazaɓar Ijesha Oriade/Obokun na Jihar Osun, Wole Oke, ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An ce, ‘yan bindigar sun yi galaba a kan masu gadin fadar, inda suka tafi da sarkin zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.   Da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ‘yansandan jihar Kogi ta ce, an fara gudanar da bincike, inda ta ce rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an tsaro da ‘yan banga na yankin sun fara farautar ganowa tare da kubutar da sarkin.   Sai dai shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Hon. Tosin Olokun ya yi Allah-wadai da sace Sarkin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da jagoran da ya kafa majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin ya aike masa, yana mai karfafa gwiwar cibiyar da kamfanoni mambobinta, da su samar da sabbin gudummawar raya alakar Sin da Denmark, da kawancen Sin da Turai, kana su zurfafa hadin gwiwa na cimma moriyar juna tsakanin sassan. Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cibiyar da kamfanoni mambobinta za su ci gaba da taka rawar gani, wajen karfafa cudanya tsakanin Sin da Denmark da ma tsakanin Sin da Turai baki daya, kana su ba da gudummawa wajen bunkasa fahimtar juna da abota, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin sassan. A baya bayan nan, a matsayinsa, da kuma...
    A wasu rahotanni sun ce an kashe makiyayi guda ɗaya da shanu sama da 100 a wasu hare-hare da aka kai hari kan makiyaya a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato. Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya wuta a lokacin da suke kiwo, wanda ke nuna rashin tsaro a yankunan da aka daɗe ana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ke janyo asarar rayuka. Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na...
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara jihar. A watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya mari Minista Tuggar a cikin mota yayin da suke kan hanyar zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi. Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba — Gowon Amma Mataimakin Gwamnan ya musanta faruwar hakan. Da yake zantawa da BBC Hausa, Tuggar ya ce saɓanin ya samo asali daga wajen Gwamna Bala Mohammed ba daga wajen mataimakinsa ba. “Muna cikin mota tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa,” in ji...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƴan majalisar tarayya guda biyu daga jihar Kano, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun sanar da barin jam’iyyar NNPP zuwa APC a yayin zaman majalisar ranar Alhamis, suna mai nuni da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar. Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun ficewarsu a zaman majalisar, inda ya bayyana cewa Usman na wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya, yayin da Sani na wakiltar Karaye/Rogo. Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC Gwamna Yusuf Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Jerin Gidajen Kwankwasiyya, Amana Da Bandirawo  Ko da a kwanan baya ma Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da wasu  sun fice daga jam’iyyar NNPP, su ma dai sun ce rikicin ne ya fitar da shi. Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje da wasu...
    Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa. ’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki. Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis ne suka samu kira daga Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Jigawa game da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Dutse, domin gudanar da bincike.      
    A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini. Dr. Baka’i ya yi ishara da nauyin da ya rataya a wuyan dukkanin wadanda suke da hannu a fadace-fadacen da suke faruwa a cikin babban birnin kasar ta Libya, sannan ya bukace su da su taimaka wajen dawo da zaman tsaro a cikin kasar. Haka nan kuma ya bukace su da su koma kan teburin tattaunawa mai maimakon amfani da karfi, su kuma kaucewa bai wa kasashen waje damar tsoma...
    Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da ake yi a tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na makamashin Nukiliya.  Shugaban kasar ta Amurka dai ya bayyana hakan ne dai a lokacin da yake Magana da manema labaru a birnin Doha na kasar Katar. Da yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya da Rasha,  shugaban kasar ta Amurka ya kuma bayyana imaninsa da kusancin kawo karshen yakin tare da cewa yana kokarin ganin an...
    A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar. Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen sama marasa matuki samfurin Mq-9 daga Amurka. Gabanin isarsa kasar ta Katar, shugaban kasar ta Amurka ya fara yada zango ne a kasar Saudiyya inda ya sami kyakkyawar tarba daga mahukuntanta, tare da kuma da kulla yarjejeniyar kasuwanci ta billiyoyin daloli. Saudiyyar ta yi alkawalin zuba hannun hajri a can Amurka da kudaden da su ka kai dala biliyan 500 zuwa biliyan 600. Haka nan...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga. A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi a ƙofar gidansa inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 100 kafin daga bisani a daidaita a kan miliyan biyar. Majiyoyin sun a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gida ne maharan suka far masa suka fito da shi daga cikin motarsu, sa’annan suka make shi da gungumen ice sa’annan suka tafi da shi. Wani makusanci ga waɗanda suka kai kuɗin ya bayyana cewa, “Bayan daidaitawa...
    Maza sun fi mata yawa wajen kamuwa da cutar. Hukumar ta kuma tabbatar cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da cutar ba daga ma’aikatan lafiya ba a wannan makon. Haka kuma, tsarin haɗin gwiwa na yaƙi da cutar zazzaɓin Lassa na ƙasa na ci gaba da aiki don tsara matakan daƙile yaɗuwar cutar. NCDC ta gargaɗi al’umma cewa ko da yake an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, har yanzu akwai barazanar cutar musamman a jihohin da ke da yawan masu cutar. Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa kiyaye tsaftar muhalli, kai rahoton alamomin cutar da wuri, da kuma nisantar ɓeraye domin su ne ke yaɗa cutar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan sahayoniyar sun yi amfani da manyan bindigogi da kuma jiragen sama na yaki. Adadin wadanda aka tabbatar da sun yi shahada ya zuwa yanzu sun haura 40. Sai dai wasu rahotannin da suke fitowa daga Gaza din sun ce, adadin shahidan ya karu zuwa 82. Jiragen HKI suna kai wa yankin na Gaza hare-hare daga kduancinsa zuwa arewacinsa cikin hauka. A Khan-Yunus ‘yan Sahayoniyar sun...
    Shirin zai kuma samar da dubban guraben aikin yi ga matasa, wanda hakan zai rage rashin aikin yi a ƙasar. Mutanen karkara da manoma da suka fi fama da matsalolin tsaro za su fi amfana da wannan mataki. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba za a bar masu aikata laifuka suke cin karensu ba babbaka ba. Ya ce gwamnati za ta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko ina a cikin Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ta ce ta gudanar da aikin bisa ƙa’ida da bin doka, kuma tana Allah-wadai da masu yaɗa ƙarya da nufin ɓata mata suna. Ƴansandan sun jaddada cewa za su ci gaba da aikinsu na yaƙi da laifi da bin doka da ƙwarewa a duk faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za ta kara ranar Laraba a birnin Bilbao. Yoro ya ji rauni ranar Lahadi a wasan da West Ham ta doke United 2-0, shi kuwa De Light a wasan Brentford ya ji rauni. Shi kuwa Heaven ya yi atisaye shi kaɗai, sai dai Jonny Evans da Toby Collyer sun yi atisaye tare da ƴan wasan United. Diogo Dalot ya motsa jiki shi kaɗai, wanda ke fatan...
    A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka Donald Trump shima ba zai halarci taron ba – duk da cewa ya nuna sha’awar halarta jiya idan har Putin zai je. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, zai kuma kasance a babban birnin Turkiyya, Ankara a yau don ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan inda ya ce zai je taron tattaunawar da Rasha a Istanbul ne kawai idan Putin ya halarta. Tun daga watan Disamba na...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi.   Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau.   Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su.   A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
    Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya.   Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki.   Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya.   An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan jihar Kano da ke niyyar gudanar da aikin hajjin bana.   Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu na gari a jihar, su kuma yi addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da hadin kan jihar Kano da Nijeriya baki daya.   Ya jaddada kudirin gwamnati na tallafa wa duk maniyyata a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki.   Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ya shawarci alhazai da su kwantar da hankulansu, su kuma maida hankali wajen gudanar da ibada.     A nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin...
    Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hukumar kula da manyan makarantu ta jihar Kaduna, ta shekarar 2025, ya zama doka. Dokar dai na da nufin daidaita harkokin gudanar da manyan makarantun sakandire a fadin jihar domin daidaita tsarin ilimin zamani.   Da yake jagorantar zaman majalissar, mataimakin kakakin majalisar Mista Henry Magaji Danjuma ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta inganta yadda ake gudanar da manyan makarantun sakandire a jihar.   Kudirin dokar ya biyo bayan gabatar da rahoton Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, shugaban kwamitin hadin gwiwa kan ilimi da shari’a, kuma wakilin mazabar birnin Zaria. Ya bayyana cewa dokar ta zama dole ne ta hanyar gyare-gyaren nan a tsarin ilimin Najeriya.   “A da, mun gudanar da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta kammala shirye-shiryen kaddamar da wani shiri na sana’ar kiwon dabbobi da ya maida hankali kan matasa, wanda aka tsara domin horarwa da samar da kayan aiki da kuma samar da kudade ga masu son noma a fadin jihar.   Kwamishiniyar Raya Dabbobi ta jihar, Misis Oloruntoyosi Thomas ta bayyana haka a lokacin da ta ziyarci sansanin wayar da kan matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, karamar hukumar Edu ta jihar.   Ta ce shirin wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Jihar ke yi na mayar da jihar ta zama wata matattarar kirkire-kirkire da kuma dabbobi.   Kwamishinan ya bayyana cewa, ma’aikatar ta hada kai da hukumar NYSC domin samar...
    Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano, domin bayar da takardar shaidar difloma ga masu amfani da shafukan sada zumunta da ke da hannu wajen tallata manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf.   Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan a karshen taron yini biyu da aka gudanar a Kano.   Kwamared Waiya ya ce horon na da nufin inganta yadda mahalarta taron ke amfani da kafafen sada zumunta wajen musayar bayanai da suka shafi ayyukan gwamnati.   “Kwas din diflomasiyyar da aka gabatar zai inganta karfin mahalarta don yin amfani da dandamali na kafofin watsa labarun yadda ya kamata wajen yada bayanai kan manufofi...
    A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi. Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje...
    Jagoran juyin juyala halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, ya zargi kasashen yamma da goyon bayan kissan kare dangin da ke faruwa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da wadanda suka shirya taro na farko don tunawa da likitoci shahidar a yanki mai tsarki na shekaru 8 tsakanin Sadam Hussain na kasar Iraqi wanda yake samun goyon bayan manya manyan kasashen duniya a lokacin da kuma jaririyar JMI a lokacin. Jagoran ya yi tir da dukkan yake yaken da kasashen yamma suke tallafawa a yammacin Asiya daga ciki har da yakin Gaza, inda HKI wacce take samun goyon bayan manya-manyan kasashen...
    Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta zama lafiya, wanda kasashen yamma suke zarginta da kokarin kere makaman nukliya. Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bayyana haka ne a gefen taro Makamashin Nukliya na kasar Iran karo na 31 wanda aka gudanar a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa babu wata cibiyar sarrafa makamashin nukliya wanda Iran ta boyewa hukumar IAEA a da ko yanzu. Kuma da akwai...
    Manya-Manyan Jami’an  gwamnatin kasar Iran da tokwarorinsu na kasashen turai uku wadanda ake kira,  E3 zasu fara tattaunawa a tsakaninsu dangane da tattaunawa dangane da makamashin nukliya tsakanin Iran da Amurka wanda ke ci gaba a halin yanzu. Kasashen E3 dai sun hhada da Faransa, Jamus da kuma Ingila wadanda suke sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015. Manufar taron ko kuma tuntubar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe uku itace sanyasu a kan hanya kan yadda tattaunawar take tafiya, da kuma yadda ake son a gabatar da sauye-sauye wa yarjeniyar JCPOA, tunda Amurka ta waresu daga wannan tattaunawar. JMI tana ganin idan har an cimma wata yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ba zai bambanta sosai...
    A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin bil\adama ya yanke hukuncin sallamar Dr. Khan Suri malami a Jami’ar Georgetown ta Amurka wanda jami’an tsaro na shige-da fice suka kama a cikin makonnin da suka gabata saboda jawabin da yayi a taron gangami na goyon bayan Falasdinawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kotun ta gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an custom da kuma shige da fice na AMurka (ICE) suka sake Dr Khan Suri daga inda suke tsare da shi makonni 8 da suka gabata, ya koma Texas inda yake zama tare da iyalansa, daga Viginia inda ake tsare da...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata suna da amincin rundunar. Nguroje ya yi gargaɗi game da yaɗa labaran ƙarya da ka iya janyo cikas ga binciken da ake yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ofishina ya cika da tarin jama’a suna ta kiraye-kiraye kan wannan mummunan sakamakon da aka samu a jarabawar JAMB ta 2025.   “ASUU za ta kalubalanci wannan sakamakon a gaban babbar kotu idan JAMB ta gaza sake duba sakamakon da kuma bai wa dalibai makin da suka cancanta.” In ji shi   Ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas da su tashi su kalubalanci abin da ya kira da rashin adalci domin hana dalibai daga shiyyar samun shiga manyan makarantu a kasar nan.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Laraba ya bayyana shirin sake gudanar da jarabawar ga dalibai da suka fito daga jihohin Kudu maso Gabas da Legas. Daga kanmu, magana ta...
    A nasa bangare kuwa, shugaba Boric ya ce, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ga kasarsa, kuma hadin gwiwarsu ya ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. Kazalika kasar Chile tana fatan yin hadin gwiwa da Sin wajen kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka da kiyaye karfin MDD, tare da kuma kare yanayin adalci na kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan.   “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya.   “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.”   Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
    Kasar Sin ta zage damtse kan wannan aiki inda ta kuduri aniyar yin ginin tashar da kayan da aka sarrafa da albarkatun duniyar wata, tare da tabbatar da cewa suna da ingancin da za a iya dogaro da su. Wannan zai zama ta harbi tsuntsu biyu da dutse guda, na farko zai saukaka sufurin jigila da kuma kula da gyaran tashar yadda ya kamata. Babban jagoran tsara aikin binciken duniyar watan, Wu Weiren ya ce kasar Sin ita ce ta farko a duniya da ta kera injin buga tubali ko bulon gini na kasar duniyar wata ta hanyar amfani da kayan aiki da aka sarrafa daga albarkatun duniyar watan. Injin yana aiki ne ta hanyar janyo makamashin hasken rana tare...
    Kasafin kudi na birnin tarayya Abuja (FCT) na shekarar 2025, kimanin naira tiriliyan 1.78 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisa, ya tsallake karatu na biyu. Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin FCT na 2025 ta wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da kudirin domin saukaka aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a babban birnin kasar. Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte Da yake karanta wasikar a zauren majalisar a ranar Laraba a Abuja, Akpabio ya bayyana cewa, gabatar da takardar ya yi daidai da sashe na 299...
    Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba, don haka ne Amurka ke haddasa matsalolin tattalin arzikin Iran. A gefen taron majalisar ministocin a yau Laraba, Araqchi ya bayyana cewa, abin da Trump ya fada game da kasashen yankin da suke son bin hanyar samun ci gaba da wadata shi ne, a hakikanin gaskiya irin tafarkin da al’ummar Iran suka bi a lokacin juyin juya halinsu, da kuma tafarkin da suka zaba na...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza. Ya yi kira da a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta tare da baiwa Falasdinawa ‘yan gudun hijira ‘yancin komawa kasarsu ta gado. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin...
    Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba. A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce: Trump ya karfafa al-Julani da yin abin da ya bayyana a matsayin wani babban aiki ga al’ummar Siriya, wato sanya hannu kan yarjejeniyar kyautata alakar jakadanci da gwamnatin yahudawan sahayoniyya, a karkashin tsarin da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Morocco suka kulla alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila a shekara ta 2020. Trump ya kuma...
    Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse. Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar. Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar za ta kara inganta kula da duk wani abu mai nasaba da sarrafawa ko samarwa a bangaren ma’adanan kasa masu matukar muhimmanci, don hana fitarwa ba bisa ka’ida ba, da kuma kiyaye tsaron kasa.  Mai magana da yawun ma’aikatar wanda ya bayyana haka a yau Laraba, ya ce, karfafa yadda ake kula da fitar da albarkatun ma’adanai masu muhimmanci zuwa ketare yana da muhimmanci ga tsaron kasa da muradun ci gaba. Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025 A ranar Litinin da ta gabata ne, wani taron kasa da aka...
    A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51, ciki har da 45 a arewacin zirin Gaza. Wannan sabon tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke gudanar da ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran Falasdinawan “WAFA” ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudanci da arewacin zirin Gaza...
    Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin da jirgin sama maras matuki ciki ya yi niyyar kai wa kan mafi girman sansanin sojin ruwan kasar da sanyin safiyar Laraba, in ji wata majiyar soji. Wannan dai shi ne rana ta hudu a jere da ake kai hare-hare kan birnin Port Sudan da ke karkashin ikon gwamnati. Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta ce, jiragen saman yakin marasa matuka ciki sun kai hari kan sansanin sojin ruwa na Flamingo, kuma na’urorin kakkabo makamai masu linzami suna kakkabo makaman da aka harba. Tsawon rabin sa’a ana jin karar makaman roka masu linzami...
    Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.   “Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.”   Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabanbanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa.   “Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.”   Idris...
    Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da manyan ayyuka guda biyar, domin neman ci gaba da farfadowa tare, da kuma raya makomar al’umma ta bai daya. Masana sun bayyana cewa, jawabin da ya yi, ya kunshi shirin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, tare da ba da jagoranci kan aikin. Ban da haka kuma, yayin taron na wannan karo, an zartar da “Sanarwar Beijing”, da “Shirin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu. ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara  Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts. Ya ce...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar.   UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
    Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale. Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da...
      Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.   Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani wato BRT da aka gudanar a Kaduna.   Aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani yana da nufin inganta zirga-zirgar ababen hawa a birane, rage cunkoso, da kuma inganta rayuwar jama’ar Jihar Kaduna. Kwamishina Ma’aikatar Aiyyuka da Ababen More Rayuwa, Ibrahim Hamza ya tabbatar da kudurin gwamnati na sauya...
    Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar. Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki. Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni ta yadda shugabanci zai riƙa kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa. Domin sauke shirin, latsa nan
    A jiya ne uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matar shugaban kasar Brazil Rosângela da Silvaa wadda ta rako mai gidanta a ziyarar da yake yi a kasar Sin, suka ziyarci babban zauren nuna fasahohin nishadantarwa ta kasar Sin, inda suka kalli abubuwan dake ciki, tare da kallon wasan opera da wasu wake-waken Sin da Brazil. Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Brazil suna mu’amala da juna a fannin al’adu, kuma jama’ar kasashen biyu suna ta kara fahimtar juna, da sada zumunta mai zurfi. A nata bangare kuwa, Madam Rosângela ta jinjinawa nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu da kuma yadda ake raya al’adun kasar. Tana fatan kara sa kaimi ga yin mu’amala a tsakanin...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin  Khan-Yunus. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a...
    Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu. Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da cewa da akwai yiyuwar a kara samun saukar mamakon ruwa sama a tsakiyar kasar, nan da wasu kwanaki masu zuwa. Wannan ambaliyar dai wacce ta shammaci mutanen kasar, a lokacin da kungiyar agajin kasar ta sanar da cewa, tana da karancin kayan da ake da bukatuwa da su domin kai daukin gaggawa idan hakan ta faru. Kasar Somaliya ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a...
    A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi. Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin wakilan majalisun, kasashe mambobi. An bude taron ne dai daga jiya Talata 13 ga watan Mayu, zai kuma ci gaba har zuwa ranar 15 gare shi. Tun a jiya ne dai wakilan Iran su 4 daga majalisar shawarar musulunci ta kasar su ka isa birnin na Jakarta domin halartar taron.
    Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”. A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu. Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza. A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza. Sojojin HKI suna ci...
    Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu. CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami. Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo na musamman sun kammala a makon jiya, sannan kuma rundunar ta ƙaddamar da sabbin dabarun yaƙi da laifuka kamar sintiri a manyan hanyoyi, kai samame maɓoyar ‘yan daba, da kuma binciken motocin jama’a a wurare daban-daban. Ya ƙara da cewa rundunar tana aiki da al’umma ta hanyar amfani da tsare-tsaren ‘yansanda. Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Jihar Kogi, musamman sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.   Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.   A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC).   Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon...
    Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da dokar kafa doka da za ta samar da tsari da kula da bada izinin filaye da yarjejeniyoyin al’umma ga masu hakar ma’adanai da sauran batutuwan da suka shafi hakan.   Shugaban Majalisar Dokta Danladi Jatau, ya sanar da amincewa da kudirin a zaman majalisar a Lafiya.   Shugaban majalisar ya ce kudirin dokar idan Gwamna Abdullahi Sule ya amince da shi zai magance kalubalen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.   Shugaban majalisar ya ce sashe na uku na kudirin ya ba da umarnin kafa Asusun Raya Al’umma na CDF don inganta walwalar al’ummomin da ke hakar ma’adanai ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da ayyukan jin kai.   “Kamfanonin...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da su tabbatar da cewa Kansilolinsu sun shiga dukkan ayyukan da aka gudanar a kananan hukumominsu .   Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da kansilolin kananan hukumomi 484 daga kananan hukumomi 44 na jihar.   Taron wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati, da nufin karfafa alaka tsakanin gwamnatin jihar da majalisun kananan hukumomi.   Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa tana da hankali kuma ba ta da almundahana, kuma ba za a amince da duk wani nau’i na almundahana ba.   Ya kuma bukaci kansilolin da su yi aiki tukuru don ganin sun rike amanar...
    Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram na Ƙaramar Hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata. Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria A wani ƙuduri da mai tsawatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar a ranar Talata,...
    A yanzu haka ana zargin wasu dakarun sojin sun ɓace tun bayan kai harin na ranar Litinin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe Zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to...
    Wata majiyar kuma ta buƙaci dakarun Nijeriya da su ɗauki matakin gaggawa. “Har yanzu ‘yan ta’addan na riƙe da sansanin. Ya kamata a gaggauta dawo da zaman lafiya a yankin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare. Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake wani Jawabi a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran. Janar Salami yana wannan maganane bayan da shugaban kasar Amurka Dunal Trump wanda yake ziyarar wasu kasashen larabawa a yankin yammacin Asiya, na cewa idan an kasa cimma dai-daito tsakanin Iran da Amurka a tattaunawa kan shirinta na makashin nukliya to Iran ta shiryawa yaki. Salami ya kara da cewa sun san...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata. Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya. Wannan yana zuwa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya  wadanda suka hana da  nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...
    A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa. An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Ya ce, “Samar da motocin aiki ga jami’an tsaron zai bayar da ci gaba wajen sawwaƙa masu zirga-zirga, kai ɗauki a kan lokaci da ƙara ƙarfafa masu gwiwa wajen samar da tsaro da bin doka da oda. “Wannan taro na yau, wani ci gaba ne na ƙoƙarin gwamnatina wajen ƙarfagawa, tare da inganta ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a duk faɗin jihar. “Wannan kuma yana ɗamfare ne da alƙawuran da muka yi, tare da jajircewar mu wajen samar da duk abin da za mu iya don tunkarar dukkan nau’o’in rashin tsaro, samar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar mu. “Wannan ƙoƙari namu yana ƙara nuna hobbasan gwamnatin mu wajen ƙarfafa wa jami’an tsaron mu don...
    Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...
    Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman.   Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan dake addabar al’umma masu karamin karfi.   Ya ce, “tun lokacin da cibiyar ta fara ayyukan jinkai don yaki da cutar makanta a Nijeriya, cikin watan Oktobar 2019, KSrelief ta gudanar da gwaje-gwajen idanu sama da 218,000, da gudanar da tiyatar idanu sama da 21,000, kuma da bayar da tallafin tabarau sama da 45,000 ga al’umma.   “KSrelief ta samu karbuwa a matsayin daya daga...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu. Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya ‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram...
    Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare. Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine. Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa ​​a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya. Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki. Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi girma a tarihi. ” Wannan yarjejeniya, wacce wani bangare ne na babban kunshin alkawurran saka hannun jari – da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 600, a cewar gwamnatin Amurka – za ta ba wa masarautar Saudiyya damar sayen “kayan aikin soja daga kamfanonin tsaron Amurka goma sha biyu,” musamman a fannin tsaron sararrin samaniya, makamai masu linzami, tsaron teku da tsarin sadarwa. A wani...
    A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar. An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi. Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa. Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.
    Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan...
    Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja. Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi.   “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri.   “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141.   “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...
    Na hudu, zaman lafiya, Sin na fatan tabbatar da shawarar tsaro ta duniya tare da bangaren Latin Amurka, kuma za ta samar musu horo a bangaren aiwatar doka da shari’a bisa bukatunsu. Na karshe, muradun jama’a, inda karkashin haka Sin za ta samarwa dalibai 3500 na mambobin kawancen kasashen Latin Amurka wato CELAC tallafin kudin karatu cikin shekaru 3 masu zuwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba. A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba. Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14. Tukur Umar, ya bayyana...
    Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya. Kudurin dokar na neman wajabta yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
    Kwamandan rundunar Amotekun a Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana ƙoƙarin ceto Adepoyigi. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ondo, Olushola Ayanlade, shi ma ya tabbatar da sace shugaban na APC, inda ya ce an sace shi a gonarsa da ke hanyar Ifon-Owo. Ya ƙara da cewa DPO na Ifon tare da mafarauta, ‘yan sa-kai da sojoji sun fara bincike domin gano inda aka kai shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daidai lokacin da  sake bude yaki a Gaza ya cika kwanaki 57,sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare akan al’ummar Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama. Cibiyar watsa labaru ta Falasdinu ta sanar da cewa; Sojojin na HKI sun kai hare-hare masu yawa a sassa mabanbanta na gaza wanda ya fara tun daga watan Maris, da hakan ya kara jefa Falasdinawa cikin wahala, bayan yunwar da suke fama da ita. Da safiyar yau Talata sojojin na HKI sun kai hare-hare  sau 3 a garin Abasan a gabashin Khan-Yunus. A cikin birnin Gaza kuwa sojojin na HKI sun baje wasu gidaje da kasa a karo na uku. A garin Khan-Yunsu wani matashi mai suna Amid...
    A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
    A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin wanda ya sami halartar masana wannan fage. Wasu batutuwa da za a tattauna a wurin taron sun kunshi; Bututun tace sanadarin Uranium, shi kanshi makamashin da kuma hanyoyin tafiyar da da kula cibiyoyin dake aikin tace da sarrafa makamashin na Nukiliya.
    Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa. Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba. Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Jami’an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp