Aminiya:
2025-11-22@12:16:23 GMT

Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura

Published: 15th, April 2025 GMT

Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.

Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa.

Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.”

Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta tabbatar wa BBC cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu a harin ya kai mutum 51.

“Maharan sun shiga ne suka buɗe wuta ne kan mutane suna barci suka ji ruwan harsasai.

“Sun kashe mutane a gidaje da kuma kan titi, yanzu an ƙidaya gawarwaki 51, in ji Sunday Abdu, Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Filato.

Bayanai sun ce wasu mahara ɗauke da makamai ne suka yi harbin kan mai uwa da wabi a ƙauyukan Zike da Kimakpa, inda nan take mutane 47 suka mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata waɗanda aka kwantar da su a asibiti.

Wannan hari ya zo ne kwanaki 10 bayan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40 a yankin.

Dole a ɗauki mataki — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da ƙazamin harin, yana mai kira Gwamna Caleb Mutfwang da ya ɗauki matakin magance matsalar da ake samu.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.

Shugaban ya aike da saƙon jaje ga gwamnatin Jihar Filato da kuma jama’ar jihar, tare da kiran gwamnan jihar da ya ɗauki matakan da suka dace na siyasa wajen warware rikicin da kuma samar da dawwamammen zaman lafiya.

Yayin da yake bayani kan muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar, Tinubu ya buƙaci son juna da haɗin kai ba tare da nuna banbancin ƙabila ko kuma addini ba.

Shugaban ya buƙaci shugabannin addinai da na siaysa a ciki da wajen jihar da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen irin waɗannan hare hare da kuma ɗaukar fansar da ake gani, waɗanda ke jefa al’ummomi cikin tashin hankali.

Tinubu ya ce ya zama dole rikicin Filato da ya samo assali daga rashin fahimtar juna tsakanin kabilu da kuma addinai ya zo ƙarshe, yayin da ya ce ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike na haƙiƙa domin gano waɗanda ke ɗaukar alhakin rikicin domin gwamnatinsa ba za ta amince da hare-haren ramakon ba.

Baya ga hukunta waɗanda suke da hannu a rikicin, shugaban ya ce ya zama dole ga shugabannin siyasar jihar, a ƙarƙashin Gwamna Caleb Mutfwang da su magance assalin rikicin dake tsakanin jama’a.

Tinubu ya ce wannan rikici na tsakanin al’umma na sama da shekaru 20, kuma ba za a iya kaucewa dalilan da ke haifar da su ba, don haka ya zama wajibi a tinkare su ta hanyar adalci.

Cikin waɗanda aka kashe har da yara da tsofaffi — Amnesty

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Amnesty International ta yi kakkausan Allah wadai da kisan aƙalla mutum 51sakamakon harin ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Zikke.

Amnesty ta koka kan cewa da yawan waɗanda abin ya shafa sun kasa tserewa — ciki har da yara da tsofaffi — wanda sakamakon hakan ‘yan bindigar suka yi musu kisan gilla suka bar su cikin jini kace-kace.

“Dole ne a binciki gazawar hukumomi kuma a daina yi musu uzuri saboda yadda wasarere din da suke yi wa sha’anin tsaro ke haifar da waɗannan munanan hare-hare, makonni biyu bayan kashe mutum 52,” in ji Amnesty.

Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ɗin ta ƙara da cewa “yin Allah kawai da wadannan munanan hare-haren bai wadatar ba kuma dole ne a nuna jajircewar kare al’umma ta hanyar tabbatar da adalci.

“A yayin da Shugaba Tinubu ke ikirarin cewa gwamnatinsa tana sanya sabbin matakan tsaro don magance ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, hare-hare na bayan nan a jihar Filato na nuna cewa dukkan matakan tsaron da ake ɗauka ba sa aiki,” ta ce.

Ƙungiyar ta ba da alkaluma na yawan mutanen da aka kashe a Jihar Filato daga Disamban 2023 zuwa Fabrairun 2024, inda ta ce an kashe mutum 1,336.

Daga cikin wadanda aka kashe 533 mata ne sai yara 263, sannan maza manya 540.

Kazalika ta ce fiye da mutum 29,554 ne suka rasa matsugunansu, daga cikinsu 13,093 yara ne yayin da mata 16,461 suka rasa matsugunansu.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Filato a jihar Filato a Jihar Filato

এছাড়াও পড়ুন:

Zaman Majalisar Amurka Kan Zargin Kisan Kiristoci A Najeriya

Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya.

Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya ƙunshi ’yan majalisa da masu kare hakkin dan’adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula.

An shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet.

Masu magana a wajen sun haɗa da Babban Jami’i na Cibiyar Harkokin Amurka Jonathan Pratt da Mataimakin Sakataren Cibiyar Dimokuradiyya, Hakkokin Dan’adam da Ƙwadago, Jacob McGee.

Sai kuma Daraktar Cibiyar ‘Yancin Addini, Ms Nina Shea; da Bishop Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdin Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Karatun Ilimin Ƙasa da Ƙasa, waɗanda suka sha tambayoyi daga ‘yan majalisar.

Yayin da wasu mambobin suka goyi bayan ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini” da daukar mataki kan Nijeriya lokacin da suke jawabi, akwai wasu daga cikin mambobin majalisar da suka bukaci a sake duba matsayin da Amurkan ta ɗauka, inda suka ce abubuwan da ke faruwa suna da sarƙaƙiya kuma suna bukatar a duba su da idon basira.

Ko da yake Shugaban Kwamitin, Chris Smith wanda ɗan jam’iyya mai mulki ta Republican ne kuma yana wakiltar Jihar New Jersey, yayin da yake jawabin bude taron ya bayyana cewa zaman yana da muhimmancin gaske, don Amurka ba za ta zuba ido kan abubuwan da suke faruwa a Nijeriya ba, kuma hakan ne ya sa yake yawan kira kan cewa akwai bukatar a dauki mataki kan ƙasar.

Sai dai wasu ’yan majalisar dokokin Amurka ba su goyi bayan matsayin Shugaba Trump kan cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya ba.

’Yar majalisar wakilai ’yar jam’iyyar adawa ta Democrat Pramila Jayapal ta ce ba ta goyon bayan daukar matakin soji a kan Nijeriya, inda ta bayyana cewa Nijeriya tana da matukar muhimmanci ga Amurka da ƙasashen Afirka.

Ta ce kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya ba Kiristoci kawai yake shafa ba, inda ta ce ana kashe hatta mabiya sauran addinai a kasar.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno
  • Zaman Majalisar Amurka Kan Zargin Kisan Kiristoci A Najeriya
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
  • Araqchi: Iran Ta Shirya Tsaf Fiye Da Kowanne Lokacin  Musamman Bayan Yakin Kwanaki 12
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas
  • Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka
  • Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano
  • Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa