Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar
Published: 15th, April 2025 GMT
Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar.
Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun da ke sintiri sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka je daga yankin Falmey.
Kazalika ranar Alhamis ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kama ‘yan bindiga 12 a ƙauyen Jagada da ke yankin Diffa.
TRT ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki a ƙauyen kuma suka fara yi wa mutane ƙwace.
Ana cikin haka ne mutane suka kira dakarun tsaron da ke ƙauyen Kablewa mai maƙwabtaka kuma dakarun suka kai wa mutanen ƙauyen Jagada ɗauki, inda suka yi nasarar kama 12 daga cikin maharan tare da ƙwace bindigogi biyu ƙirar AK47.
Domin ƙarfafa tsaro a ƙauyen da kuma hana ramuwar gayya daga ‘yan bindigar, an samar da ‘yan sintiri na dindindin da suke sun yawo a cikin ƙauyen.
An garzaya da mutane biyun da suka ji rauni a harin asibitin Kablewa inda a yanzu suke samun kulawa.
Har wa yau, dakarun Nijar sun yi nasarar kama mutum biyu masu yi wa ISWAP safarar kayayyaki a yankin Diffa.
Waɗannan nasarorin na zuwa a lokacin da sojin ƙasar ke ƙoƙarin katse hare-haren ‘yan ta’adda da ƙasar ke fama da su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga dakarun tsaron yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi
Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.
Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin.
An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Zanga-zanga ta ɓarke a KamaruBayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin.
“Sun ɗauka cewa Fulani ne suka kashe ɗan sa-kan, sai suka kai musu hari a sansaninsu.
“Mutum sama da goma aka kashe, har yanzu ma suna ci gaba da neman wasu da ba a gani ba.”
Majiyar ta ƙara da cewa, Shugaban Ƙasa na ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu labarin lamarin ba a lokacin, amma ya yi alƙawarin binciko gaskiyar abin da ya faru.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai waiwayi wakilinmu ba.