Gaza: Mutane 38 Sun Yi Shahada A Yau Litinin
Published: 14th, April 2025 GMT
Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah.
Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya.
‘Yan’uwan 6 da su ka yi shahadai, suna aiki ne da wata kungiyar agaji da take rabawa ‘yan hijira kayan abinci da sauran na bukatunsu na yau da kullum.
Sojojin HKI sun fitar da wata sanarwa da a ciki su ka riya cewa, wadanda su ka kai wa harin suna Shirin kai musu hari ne.
A jiya Litinin da marece sojojin HKI sun rushe wasu gidaje a yammacin garin Rafah a kudancin zirin Gaza.
A yammacin sansanin ‘yan hijira dake yammacin Khan-Yunus, jirgin sama maras matuki na HKI ya kai hari da hakan ya yi sanadin shahadar mutane biyu,kmar yadda su ka kashe shugaban ‘yan sandan yankin yammacin Khan-Yunus.
Wata sanarwa ta rundunar sojan HKI ta ce, a cikin kwanaki biyu da su ka gabata sun kai hare-hare ta sama har sau 90 a fadin yankin Gaza.
A wani labarin na daban, sojojin HKI sun gargadi mazauna unguwanni daban-daban a kudancin Khan-Yunus da su fice daga cikinsu, saboda za su rusa su. Unguwannin da gargadin ya shafa sun hada Qizan-al-Najjar, Abu Rashwan, Assalam da Manarah. Sai kuma unguwannin Qarin, Ma’an, Batan-al-Yasmin da Fakhari. Haka nan kuma Bani Suhailah ta kudu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar.
A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu.
Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya?
Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan