Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
Published: 15th, April 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40.
A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato.
Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon bambancin addini da kabila.
Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai domin kawo karshen ramuwar gayya da rikice-rikicen da suka jima suna addabar al’umma.
“Ya zaman wajibi a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin al’umma a Jihar Filato wanda ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin kabilu da addinai daban-daban.” In ji Shugaba Tinubu.
“Na umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan rikici, da gano wadanda ke da hannu a shirya wadannan ayyukan tashin hankali. Ba za mu amince da wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba. Ya isa haka.
Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba Gwamna Mutfwang da Gwamnatin Jihar Filato goyon baya wajen karfafa tattaunawa, inganta zaman tare, da tabbatar da adalci don magance wannan rikici har abada.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jihar Filato
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.
Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.
Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.
Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.
A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.
Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.