Wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi
Published: 28th, August 2025 GMT
Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar Sin ce.
Mai riƙon muƙamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Solomon Atang Hallet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi, kuma ana ci gaba da bincike tsakanin rundunar soji da ta ’yan sanda.
Shaidun gani da ido sun ce, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan sallar Magrib, lokacin da sojoji suka dakatar da wata mota da ke ɗauke da ma’adinai daga wurin haƙar Yalo.
Sai dai direban motar ya biris da dakatarwa ya ƙi tsayawa a shingen da sojojin suka kafa, lamarin da ya sa aka biyo shi har cikin garin Futuk.
A nan ne aka samu hatsaniya tsakanin sojojin da ɗan sandan da ake zargin shi ne yake rakiya motar.
Bayanai sun ce a lokacin da cacar baki ta ɓarke, sai ɗan sandan ya ɗauki bindiga ya harbi shugaban tawagar sojojin a baya, inda aka yi nasarar cafke shi tare da karɓe bindigar, yayin da direban motar ya tsere.
Wata majiya ta tabbatar da cewa motar na ɗauke da ma’adinai masu daraja da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba, tare da zargin cewa ɗan sandan na rakiya ne a wajen aikin.
An garzaya da sojan da aka harba zuwa asibiti a Gombe, amma daga baya ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.
Mazauna yankin Futuk sun ce ƙarar bindigar ta firgita jama’a, inda mazauna da ’yan kasuwa suka rufe shaguna suka gudu gida saboda fargabar tashin hankali.
Wani babban jami’i a Alkaleri ya yaba wa sojojin da suka kai zuciya nesa ba tare da sun ɗauki doka a hannunsu ba, sai dai sun tabbatar da kama ɗan sandan da motar.
Duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya cia, domin bai ɗaga kira ko amsa saƙonni ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Wasu mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki zargin shiga jami’an tsaro cikin harkar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, suna mai cewa lamarin na iya zama barazana ga tsaro da zaman lafiya a jihar.
A halin yanzu, kwamishinan ’yan sandan jihar ya ziyarci kwamandan rundunar soji a Bauchi, Birgediya-Janar U.J. Simon, domin kwantar da hankali da tabbatar an gudanar da sahihin bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi ɗan sandan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.