Xi Jinping Zai Ziyarci Kasashen Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
Published: 11th, April 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata.
Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Ya Yi Kira Ga Jama’a Su Yi Rijista Kuma Su Karɓi Katin Zaɓe
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, Yusuf Shuaibu Imam, ya yi kira ga mazauna yankin da su ziyarci ofisoshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin yin rijistar zaɓe da kuma karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC).
Imam ya yi wannan kiran ne yayin da yake kaddamar da jerin ayyukan raya al’umma a mazabar Tudun Wada da Gama.
Ya jaddada muhimmancin matasa, musamman waɗanda suka kai shekaru 18 a kwanan nan, da kuma waɗanda suka rasa ko katinsu ya lalace, da su tabbatar sun yi rijista domin su samu damar shiga cikin zaɓuɓɓukan da za su zo nan gaba.
Shugaban karamar hukumar ya ce yin rijistar zaɓe hanya ce ta bai wa ‘yan ƙasa damar cika haƙƙin su na dimokuraɗiyya da kuma zaɓar shugabanni na gari masu cancanta da gaskiya.
A wani bangare na jawabin nasa, Imam ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na haɓaka ci gaban, inda ya kaddamar da ayyuka sabbi guda bakwai, wanda suka haɗa da gine-ginen magudanan ruwa da gadaje da akwaku a wasu yankuna na Tudun Wada da Gama.
Khadijah Aliyu/Kano