Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027.

A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC.

Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PSP a ranar 10 ga watan Maris, tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin ‘yan adawa ta samu gagarumar nasara.

Atiku da sauran ‘yan adawa sun bayyana cewa taron na ranar 20 ga watan Maris ya nuna kaddamar da kawancen a hukumance.

A baya dai an ruwaito a ranar 23 ga watan Maris cewa ana jinkirin tattaunawa kawance tsakanin shugabannin siyasa saboda burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku na tsayawa takara da kuma rikicin shiyya.

Majiya ta bayyana cewa masu ruwa da tsaki suna da zabi da yawa don magance duk abubuwan da lamarin ya kunsa.

Majiyar ta ce, “Akwai batutuwa da dama a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a tattaunawar kawancen, inda batun arewa da kudu shi ne babban abin da ya fi daukar hankali.

“Yawancinmu mun fahimci cewa idan muka tsayar da dan takarar kudu wanda ya cancanta kuma mai gaskiya, kayar da Shugaba Tinubu zai fi sauki. Don haka da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki, musamman na arewa, suna kira ga Atiku a kan kar ya tsaya takara, ya bai wa kawancen damar mara wa dan takarar kudancin kasar nan baya da zai yi wa’adi daya idan aka zabe shi.

“A hakika, wasu daga cikin wadannan masu ruwa da tsaki sun dagewa cewa duk wani dan takara daga kudu da za su mara masa baya dole ne ya amince da alkawarin wa’adi daya.

“Wadannan al’amura sun kunno kai, amma mun himmatu wajen magance su a lokacin da suka taso da kuma daukar nauyin ‘yan Nijeriya da dama da suke fuskantar rashin iya shugabancin APC. Manufarmu ita ce tabbatar da ingantaccen tsari wanda ke wakiltar muradun jama’a da karfafa hadin kan kawancen.”

A lokacin da aka yi yunkurin jin ta bakinsa, sakataren kungiyar hadin kan jam’iyyun siyasa ta kasa, Peter Ahmeh, ya tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki na yin la’akari da shawarar fitar da dan takara daga kudancin kasar nan tare rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta wa’adi guda.

Ahmeh ya bayyana cewa, kawancen ‘yan adawar da ke adawa da Shugaba Tinubu sun fi wadanda tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya fuskanta a shekarar 2014.

Ya ce, “Rattaba hannu kan yarjejeniyar wa’adi guda da dan takara daga kudu na daga cikin abin da ke kan teburin tattauwar, amma har yanzu ba a kammala hakan ba. Bai kai ga karshe ba.

“Peter Obi da wasu masu neman takar shugaban kasa a kudu suka cikin wannan tattaunawa. Na yi imanin cewa za a cimma matsaya nan da ‘yan makonni masu zuwa.

“Akwai zabi masu yawa a kan tebur. Mutane suna kawo sauye-sauye daban-daban, amma gaskiya har yanzu ba a cimma matsaya ba. Da zaran an cimma matsaya kan wannan yarjejeniyar, za mu sanar da al’umma.

“A bayyane yake cewa ‘yan Nijeriya da yawa sun fahimci cewa wannan gwamnati tana cutar da mu fiye da alherinta. Don haka, ‘yan Nijeriya da dama ne ke shiga kawancen. Akwai ‘yan adawa da ke adawa da wannan gwamnati fiye da yadda ake yi wa tsohon shugaban kasar Jonathan a shekarar 2014.

“Don haka, ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na kkwancen da sauran shugabannin ‘yan adawa da su ci gaba da wannan alkawari domin mu hada kai don ceto kasar nan daga gazawar APC.”

Lokacin da aka tuntubi tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku kai ji ta bakinsa kan wannan kawance, ya yi gargadi game da rade-radin da ka iya kawo cikas ga tattaunawar kawancen.

Atiku, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya jaddada cewa duk wata yarjejeniya da aka kulla za ta kasance wajibi ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar juna a fadin kasar nan kan wannan kawancen ‘yan adawa.

Sai dai kuma shugaban matasan jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya soki yunkurin da ake yi na dan kudu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta wa’adi daya, yana mai cewa lamarin ba mai yiwuwa ba ne.

Da yake mayar da martani kan kawancen ‘yan adawa, Daraktan Yada Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da yunkurin kawancen, inda ya bayyana cewa farin jinin jam’iyya mai mulki a tsakanin ‘yan Nijeriya na karuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kawance masu ruwa da tsaki ga watan Maris yan Nijeriya bayyana cewa tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
  • Kamfanin Amazon na shirin sallamar ma’aikata 600,000 don maye gurbinsu da mutum-mutumi
  • Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu
  • Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka