Aminiya:
2025-11-14@22:20:43 GMT

An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa

Published: 11th, April 2025 GMT

’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin.

Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi

“An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba, muna cikin fargaba da alhini,” in ji majiyar.

An sace Fasto Ali, mai shekara 30, daga gidansa da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar 8 ga Afrilu, ƙasa da makonni biyu da naɗa shi zuwa cocin.

Tun da farko, masu garkuwar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan ɗari (N100m) ne daga shugabannin cocin.

Ƙoƙarin Aminiya na jin ta bakin hukumomin tsaro bai ci nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ECWA Karamar Hukumar Sanga

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Tsara Birane ta Kano Ta Fara Horar da Ma’aikata Kan Dokokin Aiki

Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka.

Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata.

A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati.

Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin aikin gwamnati na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen aiki, gaskiya, da kuma ɗaukaka darajar hukumar.

Daraktan kula da Ma’aikata, Alhaji Salihi Yusuf, wanda shi ne ya jagoranci zaman horon, ya jaddada muhimmancin kiyaye ƙwarewa da gaskiya a aikin gwamnati. Ya shawarci mahalarta su aiwatar da ilimin da suka koya domin ci gaban hukumar da kuma jihar gaba ɗaya.

Shirin ya ƙunshi gabatarwa ta hanyar tattaunawa da ayyukan gwaji, waɗanda suka nufi ƙara fahimtar mahalarta game da ƙa’idojin aiki, ladabi, da kuma yadda ake ƙara haɓaka ƙwarewa da ƙwazo a wurin aiki.

Rel/Khadijah Aliyu

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
  • An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
  • Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
  • Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Dillalin Makamai A Taraba
  • MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC
  • Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo rancen N1.15bn
  • An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa
  • An Bayyana Ranar Karshe Ta Biyan Kudin Aikin Hajji Mai Zuwa
  • Hukumar Tsara Birane ta Kano Ta Fara Horar da Ma’aikata Kan Dokokin Aiki