Mayakan “Jubhatun-Nusrah’ Na Kasar Syria Sun Kai Hari Akan Iyakar Kasar Leabnon
Published: 17th, March 2025 GMT
A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul
Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku.
Kungiyar ta Tahrirush-sham ta yi amfani da makamai rokoki da atalare wajen kai hari daga kan iyaka.
Tuni dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta karyata zargin na kungiyar Tahrirus-sham.
Ofishin da yake kula da watsa labaru na Hizbullah ya bayyana cewa; Babu gaskiya a cikin labaran da ake watsawa na cewa Hizbullah tana da hannu a cikin abinda yake faruwa akan iyakar Lebanon da Syria.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa; Muna sake jaddada cewa ba mu da alaka da duk wani abu da yake faruwa a cikin kasar Syria.
Wata kafa ta watsa labarai ta kasar Lebanon ta ce; kungiyar Agaji ta “Red Cross” ta mika gawawwakin wasu mayakan kasar Syria su uku da aka kashe, ba tare da cikakken bayanin yadda aka kashe sub a.
Haka nan kuma majiyar ta bayyana cewa; an harba makamai masu linzami a cikin garin al-kasar da yake akan iyaka.
Ma’aikatar tsaron Syria ta sanar da kai hari da manyan bindigogi akan wasu garuruwa Lebanon da suke a kan iyaka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu.
A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in.
Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci na halin kaka-ni-ka-yi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kungiyar za ta bayar da nata tallafin domin taimakawa al’ummar jihar bisa halin da suka tsinci kansu a ciki.
Ali Muhammad Rabi’u