Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga
Published: 30th, July 2025 GMT
Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023.
An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda ya bayyana a gaban kwamitin ranar Talata, bayan ya bayar da hakuri kan rashin bayyanarsa yayin gayyatar da kwamitin ya yi masa a baya.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Ahmed Wadada Aliyu (Nasarawa), ya tsaya kai da fata cewa dole kamfanin ya bayyana inda kudaden suka shiga.
Ojulari dai ya ba kwamitin hakuri, inda ya ce yana bukatar karin lokaci kafin ya iya amsa tuhumar da aka yi masa har guda 19.
Ya kuma ce, “Da kadan na haura kwana 100 a matsayin shugaban wannan kamfanin. Ina bukatar karin lokaci kafin na iya zakulo bayanan da kuka bukata. Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da sauran tarin ayyuka ke jira na.
“Ni kaina ina bukatar fahimtar abubuwan da kaina kafin na iya bayar da amsa a kansu. Amma zan je na zauna da sauran ma’aikatana da suka dace mu tattauna domin bayar da abin da ake bukata,” in ji shugaban na NNPCL.
Kodayake mako hudu ya bukata, amma kwamitin ya ba shi mako uku ne domin ya gabatar da bayanan.
Da yake karin haske a kan kudaden, Sanata Wadada ya ce kudaden da ake magana a kan su rubi biyu ne, akwai Naira tiriliyan 103 da kuma Naira tiriliyan 107 da suke bukatar bayanan a kan su.
“Amma fa ba mu ce wadannan kudaden da ake magana a kan su sace su aka yi ko kuma sun bace ba. Abin da kwamitinmu kawai yake kokarin yi shi ne bincike domin gano yadda aka yi tusarrufi da su,” in ji Sanata Wadada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp