Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki
Published: 5th, April 2025 GMT
Cibiyar da ke sa ido kan tsattsauran ra’ayi da ke karkashin cibiyar ilimi ta Al-Azhar ta Masar, ta fitar da wata sanarwa da ta yi kira da a kame firaministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin mai laifin yaki.
Shafin sawtbeirut.com ya bayar da rahoto kan sanarwar da ke cewa, cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayi ta Al-Azhar, ta yi Allah wadai da tarbar da kasar Hungary ta yi wa firaministan Isra’ila, wanda ke fuskantar sammaci na kasa da kasa da kotun ICC ta bayar, ta kuma sanar da cewa: “Manufar wannan mataki shi ne tauye matsayin kotun kasa da kasa da kuma keta hurumin ta.
Sanarwar ta ce: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa alama ce ta tabbatar da adalci a duniya, kuma dole ne kasashen duniya su hada kai wajen mara mata baya wajen hukunta masu aikata laifukan yaki.
Kungiyar ta bayyana cewa: shawarwarin kasa da kasa da hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki shi ne ginshikin tabbatar da zaman lafiya da adalci, kuma mutane suna da daidaito a gaban doka, babu wani wanda yake a birbishinta.
Sanarwar ta ce: “Babu lokacin yin shiru kana bin da yake fruwa, domin yin shiru yana halasta sabbin laifuka, kuma Gaza ta kasance share fage ne kawai ga ci gaba da aiwatar da bakaken manufofi da zubar da jini, da kashe rayuka.
An fitar da wannan sanarwa ne bayan da kasar Hungary ta yi maraba da firaministan Isra’ila duk da cewa kotun kasa da kasa ta bayar da sammacin kama shi.
A watan Nuwamba 2024, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba da sammacin kama Benjamin Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.
Duk da wannan hukuncin, Netanyahu ya isa kasar Hungary inda ya gana da firaministan kasar Viktor Orban.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a harkar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai a yankin Niger Delta. Daraktan Tsaron Makamashi a Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hon. Ojukaye Flag-Amachree, ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kamfanin Pipeline Infrastructure Nigeria Limited (PINL) ya shirya a birnin Fatakwal.
A cewarsa, tuni sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka an gurfanar da su a gaban kotu. Ya ce duk wanda aka kama, komai muƙaminsa, za a hukunta shi bisa doka. Ya kuma roki shugabannin al’umma da su ja kunnen matasa da yara kada su shiga lalata bututun mai.
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A JigawaYa ce: “Muna roƙonku da ku yi magana da ‘yan uwanmu. Muna sanin mutanen da ke wannan harka, ku shawarce su su daina. Yanzu abubuwa ba kamar da ba ne. Fiye da mutum 100 tuni an hukunta su. Ko kai Soja ne, ko Janar ne, muddin aka same ka da laifi, za ka fuskanci hukunci.”
A nasa ɓangaren, Jami’in hulɗa da jama’a na PINL, Tarilah Alamieseigha, ya bayyana cewa kamfanin ya amince da bayar da tallafin karatu har guda 646 da wasu ƙarin shirye-shirye ga al’ummomi 215 da ke kusa da bututun Trans Niger Pipeline (TNP). Ya yaba da haɗin kan da ke tsakanin kamfanin da al’ummomi, wanda ya taimaka wajen bunƙasa samar da mai a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp