Jagora: Iran, Tabbas Zata Ki Amincewa Da Tattaunawa Da Kasashe Masu Girman Kai
Published: 8th, March 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Ayatullah sayyid Aliyul Kahaminae, ya bayyana cewa tursasawa kasar Iran ta shi tattauna da gwamnatin Amurka ba abin amincewa ba ne, kuma yin hakan ba zai warware matsalolin da ke tsakaninsu ba.
Tashar talabijinta Presstv a nan Iran ta nakalto Jagoran ya na fadar haka a yau Asabar a lokacin da yake ganawarsa, da shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan da alkalin al-kalan kasa Muhsen Ejei da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Bakir Qalibof da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar da dama a gidansa.
Jagoran ya kara da cewa ba matsalar makamashin Nukliya ne suke bukatar tattaunawa da Iran ba, sai dai suna su tilastawa kasar Iran ra’ayinsu, a cikin dukkan al-amuran kasar. Don haka a yanke gwamnatin JMI ba zata amince da shishigi a cikin al-amuran kasar ba.
Jagoran ya zargi kasashen Turai da rashin cika alkawulansu a cikin shirin Nukliyar kasar, sannan da yi mata kariya ba tare da jin kunya ba.
Idan su na zargin Iran da rashin cika alkawula a sherin makamashin Nukliyarta? to su, sun cika alkawula ne, a shirin shirinta na Makamancin Nujkliyar?
Don haka turawan ne suka fara saba alkawulan da suka dawkawa kasar Iran, musamman bayan da Amurka ta janye daga yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015, a shekara ta 2018.
A lokacin turawan sun sha sha’alwashin kyautata al-amura amma sun kasa cikasu.
Yace Iran ba zata taba dogaro da kasashen yamma a al-amura masu muhimmanci ga ci ga mutanen kasar ba.
Kuma irana ba zata bar duk wani abu na ci gaban kasar, don tsaron wata kasa a duniya ba.
Ya kuma zargi kasashen yamma ga ba da ya da fuska biyu, musamman kan abinda ya shafi watsa labarai. Daga karshe ya ce, Ya ce Iran ba zata bar wata kasa ta yi shishiga cikin al-amuranta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp