Leadership News Hausa:
2025-12-07@20:23:21 GMT

Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata

Published: 8th, March 2025 GMT

Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata

C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai.

5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa.

Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai. Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da shanki za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu.

6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog zaya. Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Tsimin rake Kenan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abubuwan Sha

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato

’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu.

Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura.

Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin

A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.”

Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da haka sun tafi da mata huɗu.

Sai dai ya bayyana cewa akwai wani malamin makaranta, Mustafa Malam Malam, da aka taɓa yin garkuwa da shi a baya.

Duk da cewa an biya kudin fansar Naira miliyan ɗaya da rabi, ba su sake shi ba, daga baya suka kashe shi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, ya musanta batun cewa an kai hari masallaci.

Ya ce babu masallacin da aka kai wa hari ko aka kashe limami kamar yadda ake yaɗawa a kafofin watsa labarai.

Shi ma ɗan majalisar yankin, Aminu Boza, ya ce ba su da labarin wani hari da aka kai wa masallaci a yankin.

A wani labarin kuma, ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Shallah da ke mazabar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa, inda suka kashe mutum ɗaya.

Daga nan sai suka wuce garin Barkeji, inda suka ƙone rumbunan abinci a daren ranar Asabar.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwar daga rundunar ’yan sandan jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
  • Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya
  • Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21
  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa
  • Dorinar ruwa ta kashe mutum 2, ta jikkata 6 a Gombe
  • Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu