2025-05-22@22:07:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4068

«Aikin Gwamnati»:

    “Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.   “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”   Taron ya samu halartar Ministar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025. Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe...
    Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka. Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni...
    Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chikuriwa da ke Ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa...
    Shugaban Runkunin Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirinsa na karya farashin shinkafa a Najeriya, yana mai cewa nan gaba kadan wadanda suka saye shinkafar suka boye suna jiya ta yi tsada, za su tafka mummunar asara. Dan kasuwar ya kuma bayyana cewa suna tattunawa da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan hanyoyin...
    “Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.” “Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more...
    Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta shiga rudani a ranar Alhamis bayan da aka samu rahotanni masu karo da juna game da matsayin yajin aikin da reshenta na Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi. Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya gudanar da taron manema labarai inda ya sanar da cewa ASUU-KASU ta dakatar da yajin...
    Adepoyigi an sace shi ne da ƙarfe 10:00 na dare yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa a gidansa da ke Ifon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen...
    Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan...
    Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Saudia ta kaddamarda wata manhaja don kula da lafiyan mahajjata a hajjin bana, wanda aka tarjamata zuwa harsuna 8 a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency (SPA) na fadar haka a yau Jumma’a.  Ya kuma kara da cewa harsunan da ake...
    Jakadan JMI a MDD ya bayyana cewa ranar Nakba ko musiba ga Falasdinawa, abin bakinciki ba karshen musubar ba ce sai faraway ne, don a yau shekaru 77 da suka gabata kenen da musibar da ta faru da Falasdinawa tana ci gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Sa’id Iravani yaana...
    Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa. Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya...
    Wata ƙungiyar ’yan ta’adda mai alaƙa da ƙungiyar Alƙa’ida ta ɗauki alhakin kashe sojoji 200 a ƙasar Burkina Faso. Ƙungiyar mai suna Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), ta ɗauki alhakin kai hari a Djibo, arewacin Burkina Faso, tana mai cewa ta kashe sojoji 200. Wannan ikirarin, wanda cibiyar SITE Intelligence Group mai hedkwata a Amurka...
    Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan...
    Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000.   Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da...
    Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna...
    Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC reshen shiyyar Kaduna ta gurfanar da wani Muhammad Kabir a gaban kotu tare da yanke masa hukunci, wanda ya kasance mai wallafa bidiyo a shafukan TikTok da Instagram. An gurfanar da Muhammad Kabir a gaban mai shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke...
    Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna...
    Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa. A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne...
    Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau  Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai...
    Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita. Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu...
    An karrama Injiniya Dr. Mohammed Uba da lambar yabo ta kasa ta Rootswatch ta shekarar 2025, a matsayin girmamawa bisa gagarumin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma, aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa, da kuma kyakkyawan jagoranci. An mika wannan lambar yabo ne a yau a Cibiyar Karramawa ta Kasa da Kasa da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron daji a faɗin ƙasar nan domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a cikin dazukan Najeriya. A ƙarƙashin wannan sabon shiri, za a ɗauki sama da mutane 130,000 aiki da za su samu horo na musamman da kayan yaƙi na zamani domin...
    Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai...
    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi...
    A wasu rahotanni sun ce an kashe makiyayi guda ɗaya da shanu sama da 100 a wasu hare-hare da aka kai hari kan makiyaya a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato. Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya...
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara jihar. A watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya mari Minista Tuggar a cikin mota yayin da suke kan...
    Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa. ’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki. Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis...
    A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini. Dr. Baka’i ya yi ishara...
    Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga. A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi...
    Maza sun fi mata yawa wajen kamuwa da cutar. Hukumar ta kuma tabbatar cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da cutar ba daga ma’aikatan lafiya ba a wannan makon. Haka kuma, tsarin haɗin gwiwa na yaƙi da cutar zazzaɓin Lassa na ƙasa na ci gaba da aiki don tsara matakan daƙile yaɗuwar cutar....
    Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan...
    Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi.   Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar...