2025-07-11@10:30:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2735

«Kaura»:

    A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar...
    ‘Yan sandan Tehran sun sanar da kama wani dan leken asirin kungiyar leken asirin Isra’ila ta “Mosad” a cikin daya daga tasoshin jiragen kasa na birnin Tehran. Dan leken asirin wanda aka watsa furucin da ya yi, ya bayyana cewa aikinsa shi ne kera jiragen sama marasa matuki da kuma ‘yan kananan jirage, a yammacin...
     Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu...
    Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran. Janar Musawi ya  kuma yi ishara da...
      Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.   Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu....
    Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A...
    Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da...
    Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya Rahotonni sun bayyana cewa:  Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya.  Wannan ya zo daidai da wani sintiri da...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan...
    Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki...
    Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna. Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin  majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar...
    Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta...
     Kwamitin koli na  tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran.  Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar...
    Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a...
    Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa...
    Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar...
    Mai magana da yawun hukumar raya hadin-gwiwa da sassan kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, Sin ta riga ta kaddamar da ayyuka kimanin dubu 15 na inganta kwarewar ma’aikata karkashin hadin-gwiwarta da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 180, inda aka horas da kwararrun ma’aikata...
    Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da...
    Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta. An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani...
    Hukumomi sun tabbatar da mutuwar ƙananan yara 66 a sakamakon yunwa a yankin Gaza. Yaran sun mutu a yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da madarar yara da sauran kayan abinci da sauran kayan jinƙai da ake buƙata domin ceto rayuka zuwa Gaza. Mutuwar yaran ta zo ne a daidai lokacin...
    Matsalolin Da Muke Fuskanta:                     Bayan shekar 22 da kubutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuradiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kudin kasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yakin neman zabe, makudan kudin da ake ware...
    Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin...
    To sai dai ana bibiyar kwallon kafa tsakanin magoya baya a Nahiyar Turai da Kudancin Amurka, sannan kowacce takan samar da fitattun ‘yan wasan da suke fice a nahiyar da kuma duniya a fannin kwallon kafa. Wannan yana biyo bayan zuba hannun jari da bunkasa wuraren wasan kwallon kafa da gasa mai inganci da kayatarwa...
    Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da...
    A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya...
    Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600. Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk  a...
    Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da...
    Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
    A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          ( a.s)  Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala. Iyaye mata dauke da kananan yaransu  masu watanni  6 daga  haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; A cikin kwanaki 12 da su ka gabata duniya ce ta yi yaki da Iran. Hujjatul Islam Wal Muslimin   Abu Turabi Fard, ya fara hudubarsa da mika sakon ta’aziyyar shigowar ranakun Ashura, haka nan kuma jinjina ga shahidan jamhuriyar musulunci masu daraja da HKI ta...
    Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Danata rasuwa. Alhaji Aminu Danata ya rasu yana da shekaru 94 a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
    Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga...
    Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a  birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina...
    Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei. Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan  Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba,...
    Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” ya nakalto cewa;  Tun da jijjfin safiyar yau Asabar ne tasoshin jiragen kasa da na safa-safa su ka cika makil da masu son halarta babban filin Juyi na Tehran da can ne zai zama masonin rakiyar shahidan zuwa makwancinsu na karshe. Ana iya ganin dubun dubatar mutane da su ka fito...
    A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka...
    A ranar Juma’ar nan ne wasu abubuwa da ake kyautata zaton bom ne ya kashe mutane huɗu tare da raunata wasu 21 a hanyar Katarko zuwa Goniri a Ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe. Kamar yadda rahoton ke nunawa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan ƙabilar Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa...
    Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take. Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin...
    A wani mataki na ba-zata, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa nan take. Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana dalilan rashin  lafiyarsa ne ya sa ya  ɗauki matakin murabus, inda ya bayyana cewa yana buƙatar ya maida hankali kan lafiyarsa.
    Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa...
    “Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke...
    Alhaji Sabo ya yaba wa shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Dakta Abbas Tajuddeen, na yadda a tsarinsa ake koya wa matasa sana’a da zarar sun kammala yana ba matasa kayayyaki da kuma kudade domin dogaro da kai. Ya shawarci gwamnonin arewa da su duba matsalar durkushewar kamfanin yin tamfoli da ke Zariya, wanda a...
    Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya. An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar...