2025-11-03@06:49:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1224

«Garkuwan Zabarmawa»:

    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da...
    “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
    A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida. Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda...
    Ƙungiyoyin makarantu da na addinin Musulunci a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta sassauta dokar taƙaita hawa babur daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Mauludi. Shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na Jihar, Alhaji Muhammadu Nuhu, ya ce yawancin masu zuwa wajen bukukuwan na amfani da babura...
    Dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar labanon ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanar a cikin dare a birnin berut domin nuna adawa game da shirin Amurka da HKI na neman yan majalisar dokokin kasar su amince da batun kwance dammarar kungiyar hizbullah. Bukatar , wanda manzon musamman na Amurka tom barak  ya mika, da...
    Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta...
    Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama...
    Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewa maso Gabas zuwa fadar shugaban ƙasa domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba. Ganawar  wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ta mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan da suka shafi yankin Arewa maso Gabas da suka...
    Gwamnatin Nijeriya ta bayyana goyon bayanta kan shirin mayar da rubuta Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da komfuta wato CBT daga shekarar 2026. Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi. An kama wata uwa...
    Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk...
    Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon...
    Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a...
      Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.   A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa...
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar...
    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa:...
    Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar...
    Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. ‎A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake...
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika...
    Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.   “Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari,...
    Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke zarginta da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar, tana mai cewa labarin “ƙarya ne da ‘yan adawa suka kitsa domin ɓata mata suna.” Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin. PDP...
    Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa. Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon sabbin baburan hawa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabun kananan hukumomi 12 na shiyyar Jigawa ta Arewa maso yamma wadda Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya bayar da kyauta. A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yaba da kokarin Sanatan tare da shawartar shugabannin da suka sami ababan...
    Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta...
      Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna.   Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y...
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da...
    “Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a....
    Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.   Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin...
    Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A...
    Kamfanin jirgin sama na British Airways ya hana fasinjoji 58 hawa jirginsa da zai tashi daga Abuja zuwa Landan saboda matsala da ƙofar jirgin ta samu. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa saboda dalilan tsaro. Matsalar tsaro na iya hana mu ci...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha. Shugaban  ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji...
    Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma. Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun...
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar...
    Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya. A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya...