ASCSN Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Nada Muhammad Dagaceri Shugaban Ma’aikata
Published: 15th, August 2025 GMT
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha.
Shugaban ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji Muhammad Dagaceri, a ofishinsa.
Ya tabbatar wa shugaban ma’aikatan da cikakken goyon baya da haɗin kan ƙungiyar wajen cimma manufofin da aka tsara a matsayinsa na shugaban ma’aikatan jiharta Jigawa.
“Kungiyarna sa ran yin haɗin gwiwa da zai ƙara inganta aikin ma’aikata da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.” In ji shugaban ƙungiyar.
A jawabinsa, Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana godiyarsa bisa wannan ziyara, tare da jaddada kudirin wannan gwamnati na samar da kyakkyawar alaka tsakanin ta da dukkan ƙungiyoyin masana’antu a fadin jihar.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Lafiyar Tinubu kalau – Soludo
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi.
A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba.
DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin KeffiSai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya ce Tinubu na na kalau.
“Shugaban Kasa na nan kalau, kuma cikin koshin lafiya yana kuma ci gaba da ganawa da jama’a, kuma ni ma na ji dadin tattaunawa da shi,” in ji Gwamnan.
Baya ga Gwamna Soludon, shi ma takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada da kuma Ministan Kudi Wale Edun, su ma sun je fadar don ganawa da Tinubu a ranar ta Litinin.
Gwamnan Soludo dai wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, ya yi kira ga jama’a da su yi gangamin mara wa Tinubu baya, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran bunkasa Dimokuradiyya da habaka tattalin arzikin Najeriya.
Kodayake dai ya ki bayyana ainihin abin da suka tattauna ga ’yan jarida, amma dai ya ce ganawar tasu ta yi kyau.