Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta
Published: 4th, September 2025 GMT
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana goyon bayanta kan shirin mayar da rubuta Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da komfuta wato CBT daga shekarar 2026.
Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Da yake jawabi a gaban Majalisar Dokoki da manyan masu ruwa da tsaki a wani taron wayar da kai a Abuja, Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya ce jarabawa ta tsarin CBT da za a dinga yi a duk faɗin ƙasar, zai ƙarfafa tsarin ilimin ƙasar.
Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan rubuta jarabawar WAEC ta komfuta saboda a kawar da satar amsa da kuma tabbatar da an yi sahihiyar jarabawa.
“Mun ɗau aniyar mayar da rubuta jarabawa ta tsarin fasahar komfuta a matsayin wani mataki na samar wa fannin ilimi martaba.
“An yi wannan tsari na rubuta jarabawa ta komfuta saboda a rage satar amsa da kare martabar jarabawowinmu. Hakan zai ƙarfafa darajar jarabawowinmu a cikin gida da ma ƙasashen waje.
Ministan ya ƙara da cewa, duk da cewa wasu sun nuna adawa a farko, amma gwamnati tana ganin ya wajaba a dakatar da dogato tsohon tsarin da aka saba na takarda da biro.
A nasa bangaren, Shugaban Ofishin WAEC na Ƙasa, Amos Dangut ya ce an samu nasara a wannan sabon sauyin wanda aka fara gwajinsa a kan ɗalibai masu rubuta jarabawar WAEC ta kuɗi mai zaman kanta a shekarar 2024, kuma za a ƙara bunƙasa shi a faɗin kasar.
Dangut ya bayyana cewa, za a ɓullo da tsarin yin gwaji da koya wa ɗalibai yadda tsarin yake don taimaka musu wajen fahimtarsa sosai, yana mai jaddada cewa babu wani dalibi da za a bari baya.
Dangane da abubuwan da suka shafi samar da kayan aiki da matsalolin intanet, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa WAEC ta yi nasarar gudanar da jarabawar a wuraren da ke da wahalar isa ba tare da an samu cikas ba.
Ya ƙara da cewa zuwa yanzu sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarabawar gwajin ta komfuta ya yi kyau sosai fiye da jarabawar takarda da aka saba rubutawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jarabawa WAEC rubuta jarabawar rubuta jarabawa
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.
A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar DukkuDarekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.
DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.
Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.