Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare.

A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.

 

2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa

Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta hanyoyin walwalar sojojin ta hanyar biyan su kudin alawus a kan lokaci, kyautata matsuguninsu, da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya. Wannan ya kara azama wa sojojin da suke gwabza yaki a fagagen fama.

 

3. Zamanantar da Dakarun Sojoji

Ganin bukatar gaggawa da ke akwai na zamanantar da sojojin Nigeriya, Matawalle ya samar da waraka ta hanyar samar da sabbin makamai na zamani, da jirage marasa matuki don tattara bayanai da kuma kayan ayyuka da sojoji ke bukata lokacin yaki.

Wadannan kayayyaki sun inganta dabarun da sojoji ke amfani da su ta hanyar raguwar yawan sojojin da ke rasa rayukansu da kuma karuwar nasarori a duk lokacin da aka fita ba-ta-kashi.

 

4. Raguwar sace-sacen mai da zagon kasa wa tattalin arziki.

Tattalin arzikin Nijeriya ya jima na fama da illar da ake masa sakamakon satan danyen mai a yankin Niger Delta. A karkashin jagorancin Matawalle, an samu karuwar aikace-aikacen da suka hada da hadin gwiwar sojojin ruwa wadanda suka hada da lalata cibiyoyin sace danyen mai wanda hakan ya haifar da aruwar danyen mai da ake fitar da kuma karin kudaden shiga ga kasa.

 

5. Karfafa mu’amala da hadin gwiwa a yankin Afrika da kasa-da-kasa.

Yawancin matsalolin tsaro ya kan wuce iyakar kasa, saboda haka ne Dakta Matawalle bai yi kasa a gwiwa ba wurin daukar matakan kulla kawance da makwabtan asashe irin su Chadi, da Nijar da Kamaru, da sauran kawayen kasashe irin su Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai wanda ya inganta yanda ake tattara bayanai da kuma musayar bayanan sirri. Hakan ya sa ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka ke samun wahalar samun maboya.

 

6. Karfafa kere-keren kayan yaki a gida

Bisa umurnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na tunanin dogaro da kai a fannin tsaro, Dakta Bello Matawalle ya yi kokarin agaza wa Hukumar Samar da Kayan Yaki ta Nijeriya (DICON) domin kara samar da makaman yaki a gida Nijeriya. Wannan mataki ya rage dogaro da kasashen waje da kuma karfafa tattalin arzikin tsaron Nijeriya.

Baya ga bangaren yaki, Bello Matawalle yana cigaba da jaddada muhimmancin aiki da al’umma domin dawo da tsaro. Wannan kiranye da yake yi wurin neman tattaunawa, da sasanci da kuma ayyukan cigaba a yankunan da ake rikici sun taimaka matuka gaya wajen dinke rashin yarda tsakanin jami’an tsaro da kuma fararen hula, wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.

Jagorancin Bello Matawalle ya nuna aiki ba kama kafar yaro, sabbin dabaru, da kuma kishin kasa. Nasarorinsa ya nuna irin fahimtarsa a matsalolin tsaron Nijeriya da kuma irin niyyar da gwamnati ke da shi wurin magance su.

Bashir Aliyu dan jarida ne mai nazarin al’amuran da suka shafi siyasa da tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tsaro Dakta Bello Matawalle Bello Matawalle ya wanda hakan

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
  • Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
  • Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro
  • A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
  • Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
  • Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara