Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a Gombe
Published: 6th, September 2025 GMT
Ƙungiyoyin makarantu da na addinin Musulunci a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta sassauta dokar taƙaita hawa babur daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Mauludi.
Shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na Jihar, Alhaji Muhammadu Nuhu, ya ce yawancin masu zuwa wajen bukukuwan na amfani da babura ne.
Ya ce ana kammala bukukuwan da misalin ƙarfe 10 na dare, amma dokar tana fara aiki tun 7 na yamma, don haka suka roƙi a sassauta dokar saboda muhimmancin Mauludi.
Alhaji Nuhu, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa tallafin da ya bayar wajen shirya taron, da kuma tabbatar da tsaro.
Shi ma shugaban Fityanul Islam a jihar, Sheikh Bashir Ladan, ya ce bikin Mauludi na nuni da ƙaunar Manzon Allah (SAW), kuma yana ƙunshe da addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.
Haka kuma, shugaban Majma’ul Madarasatul Islamiya, Malam Muhammad Aminu Salisu, ya ƙara da rokon gwamnati ta sassauta dokar domin kada a hana mutane halartar Mauludin bana.
Ya ce sun tattauna da jami’an tsaro kuma an tanadi matakan tabbatar da zaman lafiya a yayin taron.
Ƙungiyoyin sun jaddada cewa dokar hana hawa babura ta sa wasu jin tsoro, wanda hakan ya rage yawan mahalarta jerin gwanon Mauludi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Kira taro Tsaro a sassauta dokar
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira.
Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa.
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – ZulumA cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida wa mahaifinsa niyyarsa ta kara mata ta biyu, amma mahaifinsa ya ba shi shawarar kada ya yi hakan, yana mai danganta matsalar da halin tattalin arzikin ƙasa ke ciki.
Wannan sabani ya rikide zuwa faɗa, inda ake zargin Aminu da caccaka wa mahaifin nasa wuƙa a ƙirji, lamarin da ya jawo masa rauni mai tsanani har ya rasa ransa.
An gurfanar da Aminu da laifin kisan kai, wanda ya saba da Sashe na 221 na kundin penal code.
Ana ci gaba da shari’ar, kuma kotu ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar.