Gwamna Namadi Ya Nada Kwamishina Na Farko A Ma’aikatar Cigaban Kiwon Dabbobi
Published: 15th, August 2025 GMT
Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma.
Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba.
Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare.
“Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da dama, mun yi tuntuba da dama, kuma nan gaba kadan za a fara ganin sakamakon wannan tuntuba. Bisa wannan dalili muka ga ya dace mu kafa ma’aikatar da za ta jagoranci wannan aiki gaba.”
Game da zaben kwamishina na farko, Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa a kan kwarewar Farfesa Salim Abdurrahman.
“Mutumin da aka rantsar a matsayin kwamishina na kiwon dabbobi, kwararre ne kuma masanin a wannan fannin. Daga digirinsa na farko zuwa na biyu har na uku (PhD), duk ya yi su ne akan ilimin dabbobi. Don haka babu wani da ya fi dacewa da wannan aiki fiye da Farfesa Salim.”
Yayin da yake taya Farfesa Salim Abdurrahman murna, Gwamnan ya tunasar da shi muhimmancin wannan mukami na farko da yake rike da shi, yana mai kira gare shi da ya yi aiki domin amfanin jama’ar jihar Jigawa.
“Ina sanar da kai cewa kana daf da kafa tarihi domin kai ne kwamishina na farko na wannan ma’aikata. Don haka idan ma’aikatar ta yi tasiri ga rayuwar mutanen jihar Jigawa, tarihi zai yi alfahari da kai”.
Namadi ya yi addu’ar samun nasarar wannan ma’aikata wajen inganta rayuwar al’umma a fadin jihar.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Kwamishina kwamishina na farko Farfesa Salim jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025
Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025