Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido A Karamar Hukumar Gwiwa
Published: 16th, August 2025 GMT
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban.
Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Gwiwa.
Yace a lokacin irin wannan ziyarar, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi domin tabbatar da gudanar harkokin kananan hukumomi kamar yadda ya kamata, ta hanyar aiki da tanade-tanade da kuma ka’idojin kashe kudade.
Alhaji Aminu Zakari ya kuma lura cewar Kwamatin yana kafa kananan kwamitoci domin ziyarar gani da ido dan tantance ayyukan raya kasa a lungu da sakon karamar hukumar domin tabbatar da cin moriyar kashe kudaden gwamnati ta hanyar ayyuka masu inganci.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Gwiwa, Malam Muhammad Abubakar Zakari, ya bayyana kwarin gwiwar cewa ziyarar kwamatin za ta zaburar da shugabanni wajen kashe kudade ta hanyar da ta dace, tare da wanzar da shugabanci nagari.
Malam Muhammad Zakari ya kuma sha alwashin bada cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar ziyarar.
Kazalika, ya bada tabbacin amfani da shawarwarin kwamatin domin ci gaban karamar hukumar sa.
Sauran ‘Yan kwamatin sun hada da mataimakin shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan da wakilin Malam Madori Alhaji Hamza Adamu Ibrahim Babayaro da sakataren Kwamatin da mataimakan sa da Oditoci biyu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwiwa Jigawa karamar hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.
Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.
Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.