Iran ta yi Allawadai da kisan jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta yi
Published: 31st, August 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka na rashin bin doka da oda.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na ta’addanci, tare da jaddada bukatar daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya.
Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma yana a matsayin ramuwar gayya da nufin dakile kudurin al’ummar Yemen na tallafawa al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Sanarwar ta zo ne bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar Yaman Sanaa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar firaministan kasar Ahmed Ghaleb Al-Rahawi, a lokacin da suke gudanar da taro na gwamnati tare da wasu jami’a da ministoci.
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke bayar da gudunmawarta wajen tallafawa a al’ummar Gaza, da nufin ganin gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi dare da rana a kan mata da kananan yara a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Firayi Ministan Yemen tare da wasu ministocinsa sun yi shahada a wani harin Isra’ila August 31, 2025 Argentina: Lauyoyi sun bukaci a cafke Netanyahu a kan laifukan yaki August 31, 2025 Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar August 31, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba August 30, 2025 Larijani: Iran Tana Adawa Da Juya Akalar Siyasar Yankin Daga Wasu Masu Son Baba-Kere August 30, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Wasu Kasashen Turai Na Nuna Kyamarta Zaluncin Isra’ila August 30, 2025 Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila August 30, 2025 Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher.
Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waray tarho da takwaransa na Sudan Mohiuddin Salem a ranar Juma’a.
Na farko ya nuna damuwa musamman game da hare-hare da kisan gillar da aka yi wa fararen hula a birnin El Fasher da ke kudu maso yammacin Sudan.
Duniya ta damu matuka a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar tashin hankali a Sudan.
A ranar Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana matukar damuwa game da rikice-rikicen makamai da ake ci gaba da yi a El Fasher, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula a birnin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci