Gwamnatin Kano ta musanta karkatar da N6.5bn daga baitul-malin jihar
Published: 25th, August 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke zarginta da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar, tana mai cewa labarin “ƙarya ne da ‘yan adawa suka kitsa domin ɓata mata suna.”
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce labarin da aka wallafa a wani shafin yanar gizo a ranar 22 ga watan Agusta, wani yunƙuri ne na ɓata sunan gwamnatin da kuma lalata martabar jami’anta kafin Zaɓen 2027.
Sanarwar ta ce taƙaddamar wadda a yanzu haka tana gaban kotu ta shafi Babban Darektan Tsare-Tsare (DG Protocol) na Gidan Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, inda ta jaddada cewa nauyin da aka ɗora wa ofishinsa aiki ne na gudanarwa kawai kuma ba shi da ikon riƙon kuɗaɗen gwamnati kai tsaye.
“Dukkan kuɗaɗen da ake fitarwa zuwa ma’aikatu da hukumomi ana yin su ne bisa kasafi da tsarin kuɗin gwamnati.
“Babu wani mutum da ke riƙe kuɗin ma’akatu, hukumomi ko cibiyoyin gwamnati ba tare da dalilin da aka ware masa ba,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta bayyana cewa Ofishin Protocol aikinsa ya haɗa da shirya jigilar gwamnati, walwala da jin daɗi, masauki, tafiye-tafiyen gwamna da kuma karɓar baƙi, ciki har da jakadu da manyan baƙi. Kuma saboda irin nauyin da yake ɗauka, ofishin kan sarrafa manyan kuɗaɗe amma ƙarƙashin amincewar gwamna ne kacokam.
Sanusi Bature ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta jajirce wajen gaskiya, riƙon amana da adalci, kuma ba za ta yarda a zubar da mutuncin jami’anta ta hanyar wata farfaganda ba.
Ya zargi jam’iyyun adawa da suka ɗauki hayar masu ƙirƙirar ƙorafe-ƙorafe da yaɗa bayanan ƙarya kan jami’an gwamnatin NNPP.
Sanarwar ta kuma tunatar da yadda gwamnatin baya ƙarƙashin Abdullahi Ganduje ta kashe fiye da N20bn ta hannun Ofishin Protocol tsakanin Fabrairu da Mayun 2023, ban da wasu zarge-zargen rashawa da ake yi mata.
“Mutanen Kano har yanzu ba su manta da bidiyon dala na tsohon gwamna kuma shugaban riƙon jam’iyyar APC ba,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su kiyaye ka’idojin aikin jarida su guji zama masu ruɗar da jama’a.
Ta ce ba ta da abin ɓoyewa, kuma jami’anta a shirye suke su amsa tambayoyin hukumomin yaƙi da cin hanci duk lokacin da ake buƙata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wannan zargi ƙarya ne da ’yan adawa suka kitsa a matsayin farfaganda domin neman suna a siyasance.”
Ta jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da hankali kan mulkin nagari, tattalin dukiyar jama’a da inganta rayuwar al’umma, tare da gargaɗin ’yan adawa da cewa idan suka ci gaba da yaɗa bayanan ƙarya, za a ɗauki matakin shari’a a kansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abdullahi Ibrahim Rogo Sanusi Bature Dawakin Tofa Sanarwar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp