Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’
Published: 29th, August 2025 GMT
Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo.
A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake daga bisani Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya wanke shi daga zargi, inda ya ce ba satar kudaden aka yi ba, na aiki ne.
To sai dai jaridar ta sake yin labari mai taken “Gwamnan Kano ya kare hadiminsa barawo, ya ce gwamnatin Ganduje ma ta kashe N20bn a ofishin”, inda ta ce daga cikin kudaden da ake zargin hadimin da karkatarwa, tuni ma ya mayar da Naira biliyan daya da miliyan 100 ga hukumar yaki da rashawa ta ICPC.
Amma Abdullahi Rogo ya maka jaridar da mawallafinta a gaban kotun majistare mai lamba 15 da ke Nomansland a Kano da ke karkashin Mai Shari’a Abdul’aziz M. Habib.
Rogo dai ya maka mutanen ne tare da dan jaridar da yake aiki a kamfanin mai suna Umar Audu, yana neman ta tilasta musu su biya shi diyyar bata masa suna ta hanyar kiransa da barawon da suka yi, duk da cewa ana kan bincike kuma ba a kai ga samun sa da laifi ba tukunna.
Hakan a cewar Rogo ya saba da tanade-tanaden sassa na 106 da 107 na kundin ACJL na jihar Kano na 2019 da kuma sassa na 114, 164 da 393 na kundin manyan laifuffuka na jihar Kano.
A wani labarin kuma, kotun ta umarci Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda mai kula da shiyya ta daya ta rundunar da ke Kano da ta gudanar da cikakken bincike kan zargin bata suna da kafar yada labaran ta yi.
Umarnin kotun, wanda magatakardar kotun ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 28 ga watan Agustan 2025 ya biyo bayan karar da da Abdullahi Rogon ya shigar a gaban kotun.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ja afar Ja afar
এছাড়াও পড়ুন:
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba.
Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu kurakuransu, ya kuma saka musu da Aljannar Firdaus”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA