Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
Published: 16th, August 2025 GMT
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar.
“Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a.
“Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da suka nema, ba a samu cikakken yarda ba. Dukkan wadannan abubuwan dole ne a yi la’akari da su. Kafin wannan, majalisaun tarayya ba su da hurumin amincewa da kirkirar wata sabuwar jiha.
“Kamar yadda ake ciki a halin yanzu, babu jihar da aka ba da shawara a kirkira. Ba za mu iya tabbatar da rahotanni na karshe ba ko zartar da hukunci kan jin ra’ayin jama’a da aka hada ba har sai an kammala sauraron jin ra’ayin jama’a gaba daya zuwa lokacin da muka dawo,” in ji shi.
Ya jaddada cewa ‘yan majalisar za su ba da muhimmanci ga sha’anin kasa sama da ra’ayoyinsu a yayin yanke shawarar kan batun yin garambawu a kundin tsarin mulkin kasar nan.
“Majalisar tarayya dai wuri ne na yin dokoki da kuma kula da aikin tsarawa ko gyara kundin tsarin mulki. Muna kira ga ’yan’uwanmu ‘yan majalisa su yi amfani da wannan dama da za ta dace ga kowa da kowa.
“Muna maraba da shawarwari daga dukkan ‘yan Nijeriya da suka hada da dattawa da kwararru da shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da kungiyoyin matasa da kungiyoyin mata da kungiyoyin farar hula, har ma da ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje.
“Za a bude taron sauraron jin ra’ayoyin jama’a ga kowa, kuma kundin na karshe kan gyara tsarin mulkin kasar nan zai bayyana batutuwan da ‘yan Nijeriya suka yanke hukunci a kai, ba ra’ayin wata kungiya kadai ba.
“Manufarmu ita ce, tabbatar da duk wasu canje-canje da za a yi a kundin tsarin mulki su kasance mafi kyawu ga bukatar Nijeriya da kuma mutanenta,” in ji Adaramodu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su.
Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3A ranar Laraba, ya ziyarci ƙauyuka biyar da abin ya fi shafa; Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, inda mutane da dama suka rasa ’yan uwansu.
Bayan samun labarin hare-haren, nan da nan ya tura mataimakinsa ya je ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa.
Bayan dawowarsa Gusau, ya je da kansa ya duba ɓarnar da aka yi tare da yi wa iyalan mamatan ta’aziyya.
Ya bayyana maharan a matsayin maƙiyan zaman lafiya da ke son haifar da tsoro da rikice-rikice, sannan ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’a don kawo ƙarshen aikata laifuka a jihar.
Gwamnan, ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga ta hanyar amfani da sabbin dabaru da ƙarfafa haɗin gwiwa.
Sarkin Kauran Namoda, Dakta Sunusi Ahmad, ya yaba wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai, inda ya bayyana cewa hakan ya ƙarfafa guiwar mutanen yankin.
Haka kuma, Gwamna Lawal, ya sanar da shirin inganta rayuwar jama’a ta hanyar gyaran hanyoyi, samar da wutar lantarki, ruwan sha, da inganta sadarwar wayar salula a yankin.