Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa
Published: 16th, August 2025 GMT
Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.
Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa .
“kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”.
Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani kwamitin hadin gwiwa na jami’an tsaro yaki da masu sha da fataucin muyagun kwayoyi a jihar.
Hakazalika, ya bukaci daukacin alummar jihar musamman matasa da su kaucewa tu’ammali da muyagun kwayoyi domin Kara samum zaman lafiya a fadin jihar baki daya.
Akan, yayi Kira ga iyaye da matasa da su baiwa jami’an tsaro goyon bayan da suka kamata wajen dakile matsalar shaye-shayen muyagun kwayoyi.
Ya kuma jinjinawa kokarin Hakimin Barnawa Alhaji Kabiru Zubairu na Kara hada kan al’umma da wajen tabbatar da zaman lafiya ya Kara sanuwa a garin Barnawa Dama jihar Kaduna baki daya.
A nasa jawabin Kwanishinan Ma’aikatar tsaro da harkikin cikin gida na jihar kaduna Barista Suleman Shu’aibu ( SAN) yace zaman lafiya da Samar da tsaro yana daga cikin manyan kudurorin gwamna Uba Sani inda ya bayar da tabbacin cewa zasu ci gaba da duk Mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukuyoyin alummar jihar Baki daya.
Akan hakan, yayi Kira ga alummar jihar da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon bayan da suka kamata wajen ganin an magance matsalar bata gari Wanda hakan zai tqimakawa kokarin gwamnati na kara Samar da ayyukan ci gaba a ciki da wajen jihar.
Da yake nasa jawabin hakimin Barnawa kuma Madaucin Arewan Zazzau Alhaji Kabiru Zubairu, yace babu abunda da zasu cewa gwamnatin jihar kaduna sai Fatan alkhairi da samun nasara.
Yace alummar Barnawa zasu tabbatar da cewa su ci gaba da marawa gwamnatin Uba Sani baya domin ci gaba da aiwatar da ayyukan da takeyi na ci ga.
Anasa jawabin kwamishinan da lamuran cikin gida Barista Suleiman Shu’aibu ( SAN) yace gwamnatin jihar Kaduna bata ji dadin abinda da faru ba inda lamarin ya faru ne bisa kuskure inda Yayi addu’ar Allah ya gafartawa mamacin.
A nasa jawabin hakimin Barnawa Alhaji Kabiru Zubairu ( Badauchin Arewan Zazzau) yace tun lokacin da lamarin ya faru jami’an tsaro sun bayar da gudummawa wajen ganin an samu zaman lafiya.
‘Wannan yaro da ya rasu jika ne a wurina Saboda ‘ya ta ce ta haife shi saboda haka muna da tabbacin cewa yayi shahada ne. Wannan mataki da gwamnan jihar Kaduna ya dauka na kawo mana gaisuwa bazamu manta da shi saboda ya karrrama mu kwarai da gaske Kuma.
Suma iyayen mamacin sun nuna Jin dadinsu da irin matakin da gwamnatin jihar kaduna ta dauka na aiwatar da bincike abin a yaba ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: gwamnatin jihar Kaduna gwamnatin jihar kaduna muyagun kwayoyi jami an tsaro zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.