2025-07-07@15:59:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 76
«gyaran Hanya»:
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin...
Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da...
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa. Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy...
Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna. A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin...
Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin...
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya...
Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa. Kuma, kamfanonin kasashen...
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa....
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a...
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA). Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo. Jami’ar Jihar Kano mai kula da...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da...