Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)
Published: 1st, June 2025 GMT
Ta hanyar da za ki gano kuwa ita ce, ki kai mata ziyara ta wuni daya kuma idan kin je ki kula da yaya yanayin huldodinta da kuma gyaran jikinta suke a cikin gidanta, ta nan ne za ki fahimci matsalar rashin jituwarta da mijin na ta.
Domin ita matsalar rashin kulawa da gyaran jiki wani namiji ba zai iya bude baki ya fada ba.
Koda ita matar ma ba zai iya fada mata ba sai dai kurum ka ga ana rigima ita tana ta ganin yana yi mata wulakanci shi kuma ga abin da yake gani daban, don haka yana da matukar muhimmancin ga ma’aurata da su himmantu wajen gyara jiki ba su kadai ba, har da wanda ba su yi aure ba domin addinin musulunci ma ya zo mana da nuni na kulawa da tsafta.
Sirrin Mace
Kowacce mace ta san cewa sirri ne a tare da ita sutura al’aurarta musamman ma ga mace mai aure
Yana daga cikin sutura al’aurarta da kula da gyaranta domin ita ce babbar hanya da idan ba kya kulawa da gyara ta hakika za ki fuskanci illolo daban-daban kamar za ki ji haka kawai kina wari.
Maigida zai rika gudunki, za ki ga kina fitar da ruwa mai kazanta a yayin al’ada kuma doyi ma za ki rika yi don ko dakinki aka shiga za a ji yana ta doyi.
To amma idan kina kula da tsafta hakika duka wannan za ki ji kin rabu da shi, kuma maigida ba zai rika baya-baya da ke ba, bare har ta kai ga rabuwar aure.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp