2025-11-03@09:48:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3100
«Allura cikin ruwa»:
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunwa ta diflomasiyya da Amurka domin cimma “mafita kan batun nukiliya cikin mutunta juna. “Iran ta sha sanar da cewa ba ta taba yin watsi da diflomasiyya ba kuma,” in ji Araghchi a wata hira da akayi da shi. “Ba za...
A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila. An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin...
Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba. Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a...
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i. Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000...
Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru...
Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin Jiragen Ruwan ta kantudu. Injiniya Kayode Opeifa Shugaban...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya...
Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi. Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye...
Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya. Ali Larijani ya kara da...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje,...
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong. Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba,...
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje,...
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU, ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar. A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare. Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai. Sauke Hafsoshin Tsaro: Za...
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Kiran Da A Nisanci Siyasantar Da Kwamitin Tsaron Majalisar
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Bai kamata a yi mummunan amfani da kwamitin tsaron ba ko kuma a yi amfani da shi don dalilai na siyasa Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: An gwada Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sosai ta hanyar ayyukan...
Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya
Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora...
Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin Iran kan hadin gwiwa ya jaddada cewa: Sojojin Iran a shirye suke su fuskanci kowace barazana Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran kan Hadin Gwiwa, Rear Admiral Habibullah Sayyari, ya ce: An zabi Sojojin Iran daga cikin mafi kyawun matasa a kasar kuma suna shirye su fuskanci kowace barazana. A...
Najeriya na fama da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar jinƙai ta yunwa, talauci, da rashin abinci mai gina jiki. Rahoton Yanayin Ci-Gaban Nijeriya da Bankin Duniya ya fitar a watan Oktoba, ya nuna mutane miliyan 139 a ƙasar na rayuwa cikin talauci a shekarar 2025. Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton, da cewa...
Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami...
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasu a hatsarin mota. Gwamnatin Jihar Gombe ce, ta sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Watsa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a. Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar. An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya soki matakan ƙasashen Yamma, ciki har da harin soji da suka kai wa Iran da kuma ƙoƙarinsu na sake Sanya mata takunkumi, yana mai cewa, “A...
Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi...
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya...
‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet” Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da...
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana “nasara ƙarara” da ya samu. Yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a...
Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince a rika sauya kuɗaɗe da aka ware wasu wurare zuwa swasu idan can ya fi na farko amfani ga al’umma (virement) na naira biliyan 526 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 12 na bana, Gwamna Ahmad Aliyu, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci takunkumin maimakon mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin malla. “Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, domin...
Rasha ta miƙa wa Ukraine gawarwakin sojoji 1,000 da suka mutu a fagen daga, a cewar wata hukumar gwamnatin Ukraine da ke kula da lamurran fursunonin yaƙi. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa ita ma Rashar ta karɓi gawarwakin sojoji 31 daga ɓangaren Ukraine. Messi ya tsawaita kwantiraginsa da Inter Miami Jami’an...
Fitaccen ɗan wasan tamaula, Lionel Messi, ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Inter Miami har zuwa shekarar 2028, kamar yadda kulob ɗin ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025. Wannan sabon kwantiragin zai bai wa kulob ɗin da ma gasar MLS ta Amurka damar ci gaba da kasancewa tare da ɗaya daga cikin fitattun...
Rahotanni sun bayyana cewa Ƴan ci rani 40 daga kudu da saharar Afrika sun mutu, sakamakon kifewar kwale-kwale a kasar Tunisia, sai dai an samu nasarar ceto wasu mutum 30. Kakakin ofishin masu gabatar da kara a Tunisia Walid Chtabri ne ya tabbatar da kifewar kwale-kwalen dake dauke da mutane 70 ‘yan kudu da saharar...
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja ...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa. A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya...
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu. ...
Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin...
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki. A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin...
Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin...
Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce...
Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden...
A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump...
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Komawar Iran kan teburin tattaunawa da Amurka ya dogara ne kan cimma wasu batutuwa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta koma kan teburin tattaunawa ba matukar Amurkawa ba za su yi watsi da kwadayinsu na tsarin...
Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin...
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba. Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda...
Korarren Jami’in Gwamnatin Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Hamas Ta Samu Sukunin Kai HariIsra’ila
Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son...