2025-11-03@09:48:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3100

«Allura cikin ruwa»:

      Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.   Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana...
    Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka.  Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a...
    Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa. Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000)...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da...
    Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan...
    Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron...
    A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a...
    Kwamandan sojan Iran Amir Hatami wanda ya gana da kwamandan dakarun kare juyin musulunci Janar Muhammad Pakpour saboda tunawa da makon hadin kai, ya kara da cewa; Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran da al’ummarta sun fara aiki tukuru domin kare cikakken ‘yancin Iran.” Har ila yau, Amir Hatami ya yi ishara da...
     Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci gaba sosai a fagen nazari da binciken kayan tsaro. Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa Kim Jun Ung  wanda ya yi Magana da kamfanin dillancin labarun kasar ya kara da...
    Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar. Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula, inda suka kashe mutane 5 da suka hada da yara 3 a kudancin kasar Lebanon Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar wasu ‘yan kasar 5 da suka hada da yara uku sakamakon wani hari da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
    Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin. An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon. Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun...
    Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa....
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na...
    Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba,...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
    Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su...
    A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar...
      Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.   “Na ji wani babban ƙara har sai...
    A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran,...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
    Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar...
    Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
    Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine...
    Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da...
    Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo. “Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
    Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli...
    1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona...
    A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan...
    Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI.   Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin...
    Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa,  ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila. Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa kan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato ya ce akasarin masu kai hare-hare suna fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da Filato. Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya bayyana cewa sun gana da kabilu daban-daban da kungiyoyin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shiga tsakaninta da kasashen turai guda 3 don tabbatar da cewa sun zabi diblomasiyya da Iran mai makon fito na fito da ita. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Alhamis ya...
    Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba. Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa. Wani ya sace munduwar...
    Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata. Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana. Wata sanarwa da Benfica...
    Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan...
    Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama.  Jaridar “Ma’ariv” ta amabto wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi...
      Shugabar ma’aikata ta jihar Kaduna, Madam Jummai Bako ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da fasahar Artificial Intelligence, A.I yadda ya kamata domin bunkasa ayyukan yi da gudanar da ayyukan.   Misis Bako ta yi wannan kiran ne a wani taron bita na yini guda da ofishin shugaban ma’aikata tare...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai...