2025-11-03@04:12:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4545

«Ministan Lafiya da walwalar jama a»:

    Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa...
    Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara. Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu...
    Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa...
    Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce...
    Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka...
    A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a...
    Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan...
    Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa,...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta...
    Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu Dattawan Jihar Ribas. Mai taimaka wa Wike kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne, ya wallafa hoton ganawar a shafukan sada zumunta, inda ya ce kakakin Majalisar Dokokin jihar, Martin Amaewhule, ya halarci taron. An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa...
    Dubun dubatar mutane ne suka fito zanga-zanga jiya Asabar a sassan wasu ƙasashen Turai domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, tare da kiran a kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun kuma buƙaci a saki masu fafutuka da ke cikin ayarin jiragen ruwan nan da ke hanyar kai kayan agaji ga Falasɗinawa...
    Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cafke wasu manyan jami’anta guda 16 kan zarginsu da rashin ɗa’a da kuma saɓa ƙa’idar aiki. Darekan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron soji, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ta musamman da ya fitar a ranar Asabar. Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar...
    Iran ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki matakin haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na kasa da kasa. A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga ministocin harkokin wasanni na kasashe 57 na kungiyar ta OIC, ministan wasanni da matasa na kasar Iran Ahmad Donyamali ya bukaci...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa Palasdinawa ne kawai suke da hakkin shawara kan makomar yankin zirin Gaza, da kuma abin da suke ganin ya dace da hakan, yana mai jaddada cewa mika wuya ba dabi’ar Falastinawa ba ce. Dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump kan zirin Gaza, Sheikh...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta maganganun da ake yaɗawa cewar ya ce tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, yana da alaƙa da Boko Haram. Jonathan, ya yi wannan bayani ne kan cewar an fahimci bayaninsa a baibai, a taron ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Lucky Irabor. ’Yan sanda sun kama wanda...
    BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin...
    An kuma ce duk wani bincike da aka yi a sashen karatu da kundin tsofaffin ɗalibai bai nuna sunansa ba. Wannan binciken ya jefa shakku kan sahihancin takardun ilimin ministan, tare da tayar da ƙura kan yadda gwamnati ke tantance waɗanda ake bai wa manyan muƙaman gwamnati. Duk da cece-ku-ce da ake yi, har yanzu...
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar...
    Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko...
    A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga...
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba...
    Akwai amfani saboda watarana wani abu zai taso mai muhimmanci, iyayensa ba sa kusa za su saukaka ta hanyar kiransu. Matsalar sa lalacewar karatu, koyan dabi’un marasa kyau da masu kyau, basu ko siya musu ba laifi ba ne, amma dai a tsananta saka musu ido dan gudun baraka da lalacewa. Ya zamo kiran mai...
    Dagacin garin Kirawa a Ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno, Abdulrahman Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsere daga Najeriya zuwa Kamaru bayan harin Boko Haram. A farkon makon nan, mayaƙan Boko Haram sun kai hari garin Kirawa, inda suka kashe mutum biyu sannan suka ƙone fadarsa. ’Yan bindiga sun sace uwa da...
    Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya. Hadadden...
    “Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta...
    Nijeriya za ta zama kasa mai girma duk da kalubale — Afenifere Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta nuna kwarin gwiwa cewa kasar za ta kasance mai girma. Sakon wannan kwarin gwiwa ya fito ne daga kakakin kungiyar Afenifere, Kwamared Jare Ajayi, a ranar Asabar yayin da LEADERSHIP Sunday ta tuntube shi a Akure, babban...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar “ta bukaci janyewar dukkan sojojin Isra’ila, sannan ta saki dukkan Isra’ilawan da suke tsare...
    Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump. Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da...
    A wani sabon hari rahotanni sun ce an kashe wani manomi ɗaya yayin da wasu ’yan bindiga suka sace wasu biyar a Tungan-Gari da ke Ƙaramar hukumar Kontagora a gundumar Neja ta Arewa a jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, ’yan bindiga sun kai wa al’ummar garin hari ne da misalin...
    Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) a ranar Alhamis ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, da wa’adin aikinsu ya ƙare da marasa inganci, da jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 15 a garin Ibadan na Jihar Oyo. Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar...
    Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau. “Babban kyawun demokuradiyya...
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma...
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.   Gwamnan...
    Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar.   Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.   Ya ce an...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda...
    Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a...
    Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka...
    A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.   Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da...
    Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani...