Ban taɓa cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba — Jonathan
Published: 5th, October 2025 GMT
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta maganganun da ake yaɗawa cewar ya ce tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, yana da alaƙa da Boko Haram.
Jonathan, ya yi wannan bayani ne kan cewar an fahimci bayaninsa a baibai, a taron ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Lucky Irabor.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar, Jonathan ya ce ba a fahimci ainihin kalamansa ba.
“Ofishin Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya lura da rahotannin karya da ke yawo a wasu kafafen labarai wai Jonathan ya bayyana cewa Boko Haram sun naɗa marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya wakilce su wajen tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.
“Wannan ya sa wasu ke cewa Buhari yana da hannu a harkar Boko Haram,” in ji sanarwar.
Ya ce bai taɓa zargin Buhari da goyon bayan Boko Haram ko hulɗa da su ba.
“Muna so mu fayyace cewa kalaman tsohon shugaban ƙasa an musu mummunan fahimta. Jonathan bai taɓa faɗar cewa Shugaba Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ko yana goyon bayansu ba,” in ji Eze.
Jonathan, ya ce abin da yake nufi kawai shi ne nuna yadda Boko Haram ke amfani da dabarun yaudara da ruɗani a shekarun farko na kafuwarsu.
“Maganganun Jonathan sun kasance cikin tattaunawa mai girma game da matsalolin tsaro a Najeriya. Ya yi nuni ne da wani lokaci da wasu mutane suka yi iƙirarin cewa su ne wakilan Boko Haram, sannan suka ambaci sunayen fitattun ’yan Najeriya a matsayin masu shiga tsakani ba tare da saninsu ko yardarsu ba,” in ji sanarwar.
Ya ce Boko Haram suna amfani da sunayen mutane masu daraja domin su rikitar da jama’a, suna raba kawuna, kuma suna rage amincewar mutane ga gwamnati.
“Kalaman Jonathan sun bayyana yaudarar Boko Haram, ba zargi ba ne ga marigayi Shugaban Ƙasa Buhari ko wani mutum,” in ji sanarwar.
Jonathan, ya kuma tambaya dalilin da ya sa Boko Haram ba su daina ta’addanci ba lokacin da Buhari ya zama shugaban ƙasa, idan har da gaske sun ce shi suke so ya wakilce su.
“Idan da gaske Buhari ne wanda suke so ya shiga tsakani, me ya sa ba su daina aikata miyagun ayyukansu ba lokacin da ya hau mulki?” sanarwar ta tambaya.
Ya kuma yaba da irin ƙoƙarin Buhari wajen yaƙi da ta’addanci, inda ya bayyana cewa su biyun sun yi aiki domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
“Jonathan yana tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari, kamar kowane ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, ya yi tsaya tsayin daka wajen yaƙi da ta’addanci, har ma shi kansa sai da Boko Haram suka taɓa kai masa hari.
“Su biyun, a lokacin mulkinsu, sun yi ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan,” in ji sanarwar.
Mai magana da yawun tsohon shugaban, ya roƙi jama’a da su yi watsi da rahotanninsaboda a cewarsa ba su da ma’ana.
“Ana roƙon jama’a da su yi watsi da wannan labarai. Jonathan yana nan daram wajen ƙoƙarin ganin Najeriya ta zauna lafiya, ta zama al’umma ɗaya, kuma an bunƙasa dimokuraɗiyya.
“Ya yi imani cewa ci gaban ƙasa ya dogara ne ta hanyar bayyana gaskiya, ba yaɗa ƙarya ko labaran da za su tayar da hankali ba,” in ji sanarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Buhari Labarai zargi in ji sanarwar Shugaban Ƙasa da Boko Haram a Boko Haram Jonathan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…