Sanata Ndume Ya Yaba Wa Gwamna Zulum Kan Shirinsa Na Tura Sojoji Kirawa
Published: 5th, October 2025 GMT
Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa zuwa ƙasar Kamaru.
A wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, Ndume ya gode wa gwamnan bisa alƙawarin tura Sojoji domin kare garin da kuma amincewa da gina asibiti, da rijiyoyi, da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a yankin. Ya ce irin waɗannan matakai za su taimaka wajen dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a.
Zulum Ya Rabawa Talakawan Dikwa Tallafin Kuɗi Da Abinci Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – NdumeSanatan ya kuma roƙi mazauna yankin su ci gaba da zama cikin shiri tare da sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko aiki da ake zargin na ƴan ta’adda ne. Ya ce babu yadda gwamnati ko Sojoji za su iya kawo ƙarshen Boko Haram ko ISWAP idan ba tare da goyon bayan jama’a ba.
Ndume ya bayyana ziyarar gwamnan zuwa garin a matsayin abin ƙarfafa gwuiwa, inda ya nemi a ci gaba da samun haɗin kai tsakanin gwamnati da rundunar Soji da ƴan sa-kai domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar.
A jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024.
A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.
Ya jaddada cewa mutanen wadannan yankuna sun daɗe suna bukatar wannan aiki na hanyar.
Malam Umar Namadi ya ce titin zai ba su damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni mafi kusa cikin sauki.
Ya kuma ce yawancin wadannan hanyoyi sun kai matakin kammaluwa, kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da jerin bukukuwan kaddamar da su gaba daya.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a karkara domin saukaka samun hanyoyin shiga kasuwanni da birane.
Namadi ya bayyana cewa shirin tuntubar jama’a ya bai wa al’umma damar tattaunawa kai tsaye da gwamnati.
Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo Malam, ya ce titin na daga cikin hanyoyi 48 masu dauke da jimillar tsawon kilomita 977 da aka bayar a 2024 a kan kudi Naira biliyan 304.
Wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Abdullahi Musa da Malam Muhammad Gata, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan aiki.