Sheikh Qassem: Falasdinawa ne suke da hakkin yanke shawara kan makomar Gaza
Published: 5th, October 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa Palasdinawa ne kawai suke da hakkin shawara kan makomar yankin zirin Gaza, da kuma abin da suke ganin ya dace da hakan, yana mai jaddada cewa mika wuya ba dabi’ar Falastinawa ba ce.
Dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump kan zirin Gaza, Sheikh Qassem ya bayyana cewa shrin yana tattare da hadari, inda ya kara da cewa an gabatar da shi ta wani salo na musamman ga wasu kasashen Larabawa.
An yi ganawa tsakanin Trump da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, kuma an yi canje-canje a cikin da suka yi daidai da mahangar Isra’ila a cikin bayanin, sabanin abin da aka sanar da kasashen larabawa da na musulmi tun daga farko, inji shi.
Sheikh Qassem ya kara da cewa Isra’ila na son cimma wannan buri ne ta hanyar siyasa bayan kasa ta kasa yin hakan ta hanyar kisan kiyashi da wuce gona da iri. Ya ce abin da muka gani a Gaza cikin shekaru biyu da suka gabata wani muhimmin bangare ne na wannan aiki.
Ya kara da cewa, shirin a Zahiri na Amurka ne, amma a bayan fage na Isra’ila ne, Ya bayyana cewa ana son yin amfani da hakan ne da nufin wanke Isra’ila a idon duniya daga laifukan yaki da ta aikata a Gaza.
Ya ci gaba da cewa: “Muna fuskantar wani shiri mai cike da alamun tambaya, kuma wannan shi ne abin da wasu jami’ai a kasashen Larabawa suka fada, inda suka yi mamaki tare da neman karin haske kan shirin.” Inji shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An yi gagarimar zanga zangar goyan bayan Falasdinu a Barcelona, Rome, da Paris October 5, 2025 Malawi : Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki October 5, 2025 Hamas: Ci gaba da kai hari kan Gaza ya fallasa karyar Netanyahu October 5, 2025 Sojojin HKI Sun Bada Sanarwan Fara Aiwatar Da Shirin Trump Na Tsagaita Wuta A Gaza October 4, 2025 Janar Qa’ani: An Boye Ranar Fara Yakin Tufanul Aksa Har Haniyya Bai Da Labarisa October 4, 2025 Iran Na Shirin Cilla Tauraron Dan’adam Da Sandarerren Makamashi A Cibiyar Chabahar October 4, 2025 Iran: Gasar Fasahar Kere-kere Na Shekara Ta 2025 Zai Sami Halattar Wakilai Daga Kasashe 65 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 146 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan(a) 145 October 4, 2025 Kissoshin Raytuwa: Sirar Imam Hassan(a) 144 October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa.
Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman a matakin yanki, kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da Majalisar Dinkin Duniya, wajen matsin lamba ga yahudawan sahayoniyya da magoya bayansu da su dakatar da kisan kiyashi da kuma janyewar ‘yan mamaya daga Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi juyayin tunawa da manyan shahidan gwagwarmaya, inda ta jaddada nauyin da ke wuyan kasashen duniya na hana duk wani cin zarafi daga ‘yan mamaya, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan da yaudara da karya alkawari da sahayoniyya suke yi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci