Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna
Published: 5th, October 2025 GMT
Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa, reshen Giwa.
Rahoto ya bayyana cewa Malam Kabiru ya rasu ne yayin aikin ceto wasu mutane da ’yan fashi suka sace daga yankin Danja na Jihar Katsina.
Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa, Kwamanda Usman Taju, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, jim kaɗan bayan jana’izar marigayin.
Ya ce: “Da safiyar Asabar muka samu labarin cewa ’yan fashi sun yi garkuwa da wasu maza da mata daga Danja, suka shigo da su Giwa. Nan take muka haɗu domin ceto su.
“Mun samu nasarar ceto mata uku daga hannun ’yan fashin, amma abin baƙin ciki, ɗaya daga cikinmu, Malam Kabiru Gangara, ya rasa ransa yayin aikin.”
Usman Taju, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a kan aikin kare rayuka da dukiyar jama’a, inda ya ce hakan babban abin alfahari ne.
Ya roƙi gwamnatin Jihar Kaduna da ta taimaka musu da kayan aiki da horo, domin ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
“Haƙiƙa muna fama da ƙalubale da dama, amma hakan ba zai hana mu ci gaba da kare jama’a ba,” in ji shi.
Kwamandan ya nemi gwamnati ta riƙa kula da iyalan jami’an da suka rasu a bakin aiki, domin hakan zai bai wa sauran maharba ƙwarin guiwa.
Marigayin ya rasu ya bar mata uku da yara shida, kuma an binne shi a ƙauyensu na Gangara, a Jihar Kaduna.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan fashin daji kwamanda maharba Maharbi Jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno.
Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri.
Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.”
Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna bibiyar su, inda suka kashe mayaka biyar tare da tilasta wa sauran tserewa.
Soja ya harbe matarsa, ya kashe kansa a Jihar Neja Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoniKayayyakin da aka kwato sun haxa da bindiga kirar AK-47, alburusai, wuqa, da wayar hannu.
Uba ya qara da cewa “Babu asarar rayuka ko asarar kayan aiki da sojojin mu suka yi.”
A wani samamen kuma a hanyar Gajiram Bolori – Mile 40 – Gajiganna, sojoji sun yi arangama da mayakan Boko Haram a kusa da kauyen Zundur, inda suka kashe ’yan ta’adda hudu tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su daga Guzamala.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da wata mota, sabbin wayoyin hannu guda biyu, man fetur lita 30, da tsabar kudi da suka kai Naira miliyan 4.35.
Binciken farko ya nuna cewa ’yan ta’addan sun bukaci naira miliyan 2 da wayoyi biyu a matsayin kudin fansa ga dan uwan wadanda suka kama kafin sojojin su kai dauki.
Laftanar Kanar Uba ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka matsin lamba kan ’yan ta’addan tare da hana su sakat.