Aminiya:
2025-10-13@15:47:32 GMT

Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki

Published: 5th, October 2025 GMT

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cafke wasu manyan jami’anta guda 16 kan zarginsu da rashin ɗa’a da kuma saɓa ƙa’idar aiki.

Darekan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron soji, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ta musamman da ya fitar a ranar Asabar.

Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar Getso ya rasu Ban taɓa cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba — Jonathan

Duk da cewa sanarwar ba ta bayyana sunayen jami’an da aka kama ba, sai dai ta ce binciken da aka gudanar ya danganta laifuffukan su da gaza cin jarabawar samun ƙarin girma da kuma wasu dalilai na daban.

Kakakin sojin ya ce ana tsare da waɗannan jami’ai saboda tuhumar da ake musu, kuma tuni wasu daga cikin su suka fara fuskantar tambayoyi daga masu bincike kamar yadda dokokin soji suka tanada.

Gusau ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun soji kamar yadda doka ta tanada.

Kazalika, ya jaddada cewar rundunar sojojin ƙasar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri da zai ɓata mata suna ba, ko kuma yi mata zagon ƙasa kamar yadda dokar ƙasa ta sanya su a ƙarƙashin dimokuradiyya.

Kakakin ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rundunar Sojin Nijeriya kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno

Ana fargabar sojoji da dama sun rasu yayin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke Ngamdu, a Ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kai wa sojojin hari a sansanin da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya

Biyo bayan harin, sojoji sun rufe hanyar Ngamdu har zuwa ƙarfe 11:20 na safe, wanda hakan ya sa matafiya suka maƙale na tsawon lokaci.

“Na tashi daga Damaturu da sassafe ina fatan isa Maiduguri kamar ƙarfe 9 na safe, amma da na isa Ngamdu sai muka tarar da hanya a rufe,” in ji wani matafiyi.

“Jami’an tsaro sun ce mu yi haƙuri saboda an samu matsala a hanya. Daga baya mazauna yankin suka ce Boko Haram ne suka kai wa sojoji hari tare da kashe wasu daga cikinsu.”

Wani mazaunin yankin ya ce mayaƙan sun kai wa sojojin hari ba tare da tsammani ba.

“Harin ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin ’yan ta’addan su tafi, amma sun kashe sojoji kuma sun ji wa wasu rauni,” in ji shi.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar harin, amma ta ce ba a rasa rayuka da yawa kamar yadda aka yaɗa ba.

“‘Yan ta’addan sun yi ƙoƙarin yi wa sojojin kwanton ɓauna, amma sojojinmu jarumai sun yi tsayin daka.

“Wasu daga cikinsu sun ji rauni an kuma kai su asibiti, amma an kashe ’yan ta’adda da dama,” in ji majiyar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
  • Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya
  • Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno